Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Gobe za’a cigaba da shari’ar Mustapha Inuwa da Mahdi Shehu a kotun Katsina
Gobe za’a cigaba da shari’ar Mustapha Inuwa da Mahdi Shehu a kotun Katsina

Gobe za’a cigaba da shari’ar Mustapha Inuwa da Mahdi Shehu a kotun Katsina

1

Gobe za’a cigaba da shari’ar Mustapha Inuwa da Mahdi Shehu a kotun Katsina

Babbar Kotun Sauraren Daukaka Kararraki ta Jihar Katsina ta tsaida gobe Litinin 27/9/2021 don ci gaba da karar da Mahadi Shehu ya daukaka yana kalubalantar ingancin hanyar da aka bi wajen sada shi da sammaci dangane da karar da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Dr Mustapha Muhammad Inuwa ya kai shi a gaban Babbar Kotun Kotun Shari’ar Musulunci ta biyu dake nan Katsina.

Haka kuma Mahadi Shehu na son Kotun ta soke umurnin da Kotun Shari’ar ta bayar na cewa a kamo shi, a kuma gurfanar da shi a gaban ta domin ya kare kansa daga zargin da Mustapha Inuwa ke yi masa na cin mutunci da bata suna.

A zama na karshe da aka yi kafin Alkalai su tafi hutun karshen shekara, Kotun ta karbi wasu karin takardun bayanai akan abinda ya gudana a Kotun Shari’ar wadanda Lauyan Mahadi ya yi tsambare, ya ki hadawa da su wajen shigar da daukaka karar da suka yi.

Takardun da Kotun ta amince da su sun hada da:

1. Takardar rantsuwa ta kotu (Affidavit) wacce Masinjan Kotun Shari’ar ya rantse cewa ya je Kaduna neman Mahadi a dukkan gidajensa bai same shi ba.

2. Kwafen takardar da Kotun Shari’ar ta rubutawa wata Kotu dake Abuja ta neman ta sa hannu akan sammacin da aka kai ma Mahadi a Hedikwatar yansanda.

3. Kwafen sammacin da aka kai ma Mahadi wanda Kotun ta Abuja ta buga hatimi, ta rattafa hannu a baya.

4. Kwafen Affidavit wanda Masinjan Kotu ya yi rantsuwar cewa ya baiwa Mahadi sammaci hannu da hannu a Abuja.

Idan za a iya tunawa a wani zama da Kotun ta yi a Funtuwa, Lauyan Mahadi, Barista Abbas Machika ya bukaci Kotun da kada ta karbi wadan nan takardun bayanai.

Sai dai kuma a yayin take bada bahasin Kotun a nan Katsina, Maishari’a Hajaratu Hajo Lawal ta yi watsi da wannan roko.

Tana mai cewa dukkan takardun suna da alaka da sammancin da ake magana akai, don haka batun Lauyan Mustapha Inuwa, wato Barista Abubakar Sahu Ibrahim cewa suna da muhimmanci a cikin daukaka karar dake gabanta gaskiya ne.

Don haka ta ce Kotun ta amince da su a matsayin karin takardun bayanan abinda ya gudana a Kotun baya.

Yanzu dai Kotun za ta zauna gobe a zauren Babbar Kotu ta daya dake kan titin Daura a nan Katsina da karfe 9:00am idan Allah Ya kai mu.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: