Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Mafarauta A Katsina Na Son Gwamnati Ta Basu Dama Su Shiga Daji Su Yaki ‘Yan Ta’adda 
Mafarauta A Katsina Na Son Gwamnati Ta Basu Dama Su Shiga Daji Su Yaki ‘Yan Ta’adda 

Mafarauta A Katsina Na Son Gwamnati Ta Basu Dama Su Shiga Daji Su Yaki ‘Yan Ta’adda 

0

Mafarauta A Katsina Sun Roki Gwamnati Ta Basu Dama Su Shiga Daje Su Yaki ‘Yan Ta’adda 

A Shirye Muke Mu Bayar Da Rayukanmu Dan Yaki Da Yan Ta’addan Daji Inji Ya’yan Kungiyar Mafarauta Ta Kasa Reshen Jihar Katsina Watau Hunters Group of Nigeria A Turance, kamar yadda jaridar The Fact 24 ta ruwaito.

Mataimakiyar Kwamanda Ta Kungiyar Mafarauta Ta Kasa Hajiya Umma Dauda Yar Baiwa Mai Maciji ta shaidawa Gwamnatin Jihar Katsina cewa ya’yan Kungiyar a shirye suke su sadaukar da rayukansu don yaki da yan ta’adda dake a cikin dazuka.

Mataimakiyar Kwamandar ta bayyana haka ne a lokacinda ta jagoranci sauran shuwagabannin kungiyar inda suka Kai zaiyara ga Sakataren Gwamnatin Jiha Dr.Mustapha Muhammad Inuwa.

Kamar yadda Hajiya Umma Yar Baiwa ta bayyana,ya’yan kungiyar jarumai ne da suke sana’ar Farauta kuma suka san daji.

Tace ya’yan Kungiyar sun san lungu da sako na daji dan haka shiga dazukan ba wani abu bane mai wahala a garesu.

Mataimakiyar Kwamandar tace idan dai har gwamnati zata basu dama to a shirye suke su shiga dazukan domin gamawa da yan ta’adda dake fakewa a ciki.

Tace a halin yanzu sunada mambobi sama da 100 a kowace Karamar Hukuma dake Jihar Katsina Kuma dukkansu babu wani daya tilo da bindiga ke tayarwa hankali don haka dama kawai suke jira.

Ta Kara da cewa a baya mambobinsu sunyi kokarin chafke yan ta’adda da dama kuma sun hannantasu ga Jami’an tsaro.

A nashi jawabin,Sakataren Gwamnati Dr.Mustapha Muh’d Inuwa yace batun tabbatar da tsaro nauyine da ya rataya akan kowa,a sabili da haka akwai bukatar Kara hada hannu don yaki da matsalar.

Yace Gwamnatin Masari a shirye take tayi dukkannin abinda ya dace don ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro a Jihar.

Daga nan sai ya maganta akan nasararda Jami’an tsaro samu a yaki da Yan ta’addan a halinda ake ciki a Jihar ta Katsina sai yace Gwamnati zata duba yiyuwar sanyasu a cikin batun don a gudu tare a tsira tare.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: