Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An Kama Wani Dan Kasar Nijar Da Tallafawa Yan Bindiga A Jihar Katsina
An Kama Wani Dan Kasar Nijar Da Tallafawa Yan Bindiga A Jihar Katsina

An Kama Wani Dan Kasar Nijar Da Tallafawa Yan Bindiga A Jihar Katsina

0

An Kama Wani Dan Kasar Nijar Da Tallafawa Yan Bindiga A Jihar Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta cafke wani mutum mai suna Lawal Shu’aibu, dan shekara 32, dan Maradi a Jamhuriyar Nijar da wasu mutane 4 da ake zargi da sayar da man fetur ga ‘yan bindiga da ke dazukan jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a Katsina, Gambo Isah, ya shaida wa manema labarai cewa an kama mutumin a ranar Asabar yayin da yake jigilar man cikin mota kirar Volkswagen Passat.

‘Yan sandan sun ce sauran mutane hudun da aka kama sune Sani Lawal, mai shekaru 28, na Magamar Jibia a Karamar Hukumar Jibia wanda yake kai mai shima a mota kirar Volkswagen Passat, da Abdulrashid Garba, dan shekara 50, na kauyen Daddara a karamar hukumar ta Jibia, wanda yake kai mai a cikin motarsa kirar Volkswagen Golf 3.

Kazalika, a ranar Asabar, an kama wani da ake zargi da samar da mai ga ‘yan ta’adda a cikin dajin, mai suna Shafi’u Haruna, dan shekara 25, na kauyen Anguwan Nakaba da ke karamar Hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: