Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An kama mata masu kai ma ‘yan bindiga man fetur cikin jikkunan matafiya a Katsina
An kama mata masu kai ma ‘yan bindiga man fetur cikin jikkunan matafiya a Katsina

An kama mata masu kai ma ‘yan bindiga man fetur cikin jikkunan matafiya a Katsina

0

An kama mata masu yi ma ‘yan bindiga safarar man fetur cikin jikkunan matafiya a Katsina 

Masu Mashina Muke Sayarwa Mai Idan Mun Dauka Daga Katsina – Cewar Masu Safarar Fetur Ga Yan Ta’addan Daji.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wasu mata su 3 da suke safarar man fetur zuwa Magamar Jibia domin siyarwa ga yan Ta’addan Daji.

Masu safarar man dai suna amfani ne da wata dabara ta sanya man a cikin jikkuna Kamar matafiya.

Kamar yadda Kakakin Rundunar SP Gambo Isah ya bayyana,wadanda aka chafke din dukkansu mazaunan Unguwar Malali ne a nan cikin Birnin Katsina.

Wadanda aka chafke din sun bayyana cewar suna sayar da man ne ga masu Mashina idan sun isa a Magamar Jibia inda su kuma za’a kirga kudinsu a biyasu.

Sun Kuma maganta akan dabararda suke bi wurin sayen man a gidajen mai wanda suke a nan cikin Birnin Katsina.

Idan dai za’a iya Tunawa, Rundunar Yan Sandan a kwanannan tana cigaba da samun nasara ta fuskar chafke masu safarar man fetur da sauran kayan masarufi ga Yan Ta’adda dake cikin dazuka.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: