Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Katsina Da Wasu Jihohin Arewa 6 Zasu Dauki Yan Sintiri 3000 – Inji Gwamna Masari
Katsina Da Wasu Jihohin Arewa 6 Zasu Dauki Yan Sintiri 3000 – Inji Gwamna Masari

Katsina Da Wasu Jihohin Arewa 6 Zasu Dauki Yan Sintiri 3000 – Inji Gwamna Masari

0

Katsina Da Wasu Jihohin Arewa 6 Zasu Dauki Yan Sintiri 3000 – Inji Gwamna Masari

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, yace Jihohin Arewacin Kasarnan su bakwai zasu dauki ma’aikatan sintiri guda 3000 a wani namijin kokari na shawo kan matsalolin tsaro.

Gwamna Aminu Bello Masari wanda ke magana a madadin sauran Gwamnonin Jihohin su 6 ya bayyana hakan ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki tare da Ministan Yada Labaru Da Al’adu Lai Muhammad Wanda ya ziyarci jihar Katsina domin sanin yanayinda tsaro yake ciki a Jihar.

Kamar yadda Gwamna Masari ya bayyana Jihohin sun hada da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kaduna da Kebbi da Naija gami da Jihar Nasarawa.

Gwamna Masari yace tuni suka hada kansu tare da sauran Gwamnonin domin ganin an bijiro da wannan yunkuri.

Sanin kowa ne cewa dukkan jihohin guda 7 suna fama da matsalar tsaro Wanda yaki ci yaki cinyewa Wanda hakan ya tursasa Gwamnonin fito da wannan tsari don ganin an gudu tare an tsira tare.

Alhaji Aminu Bello Masari yace a halinda ake ciki akwai sansanin Yan ta’adda sama da 150 a dazuka wanda dukkanninsu sunyi rantsuwa na rashin bijirewa shuwagabanninda suke a karkashinsu.

Ya danganta matsalar tsaron da rashin ilimi da da yawaitar yawon makamai a yankin na Arewacin Najeriya dake fama da matsalolin tsaro.

Daga nan sai ya bukaci al’umma da su bayar da goyon bayanda ya dace don ganin an cimma kyakkyawar manufa.

A nashi Jawabin, Ministan Alhaji Lai Muhammad yace ya ziyarci Jihar Katsina ne domin sanin halinda ake ciki ta fuskar matsalar tsaro a Jihar.

Yace yazo Jihar ne da kafofin yada Labarai kusan 25 Wanda zasu sanar da kasa halinda Jihar take Wanda hakan zai Kara bayar da dama ga Gwamnatin Tarayya ta Kara kawo dauki a Jihar.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: