Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA ‘Yan PDP A Gyara na da Boyayyar Manufa Inji Majigiri
‘Yan PDP A Gyara na da Boyayyar Manufa Inji Majigiri

‘Yan PDP A Gyara na da Boyayyar Manufa Inji Majigiri

0

‘Yan PDP A Gyara na da Boyayyar Manufa Inji Majigiri 

Duk Da Jihar Katsina Na Fama Da Matsalolin, Amma Sun Bar Maganar Sun Dawo Suna Cewa PDP A Gyara, Suna Da Wata Boyayyar Manufa Dai, Cewar Salisu Majigiri

Shugaban Jami’yyar PDP na jihar Katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana cewa yana mamakin wani gungun ‘yayan jam’iyyar PDP masu kiran kansu yan PDP a gyara duk matsalolin da jihar Katsina ke fama da su daban-daban da jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta jefa al’umma jihar Katsina ciki amma abun mamaki duk suna kiran kansu yan jam’iyyar adawa ba ka taba jin sun kalubalanci gwamnatin Masari ko sau daya.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai ciki har da Blueink News Hausa a gidansa dake Katsina yau Lahadi.

Shugaban Jam’iyyar Adawa ta PDP ya kara da cewa ina ganin jihar Katsina ce gaban jam’iyyar PDP, amma ba ka taɓa jin wadannan Mutane sun fito, sun soki ko sun yi kira a gyara Kura-kurai da Jihar Katsina ke fama da su ko da ta matsalar tsaro da ya ki ci yaki cinyewa a Jihar Katsina.

Idan ka ji sun soki APC a matakin Kasa ce, amma da wuyar gaske ka ji daya daga cikinsu yana sukar, kuma al’umma jihar Katsina su zama alkalai daga yau din nan, tun da suna shiga gidajen rediyo da wurin tarukka.

Majigiri ya ci gaba da cewa PDP a Jihar Katsina tarihi gare ta, tana da tushe, idan dai kana da kishinta hadin kanta shi ne gabanka. Ga inda hakkin kowane dan jihar Katsina yake, ga jama’a na fama da talauci da rashin aikin yi ga babu aikin da gwamnatin jihar Katsina ta yi, kuma ga dinbin bashin da aka ciwo wa jihar ga rashin tsaro har wani ya fito cikin PDP ya ce ita yake so a gyara ga maciji can amma ana bugun Darari, jam’iyyar da ba ta da ko Kansila a Jihar Katsina, in dai ba’a akwai wata Magana ba, a fito a gayawa al’umma jihar Katsina gaskiya.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: