Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Latest Wasu Na Son Sabi’u Tunde Ya Yi Takarar Gwamnan Katsina A 2023
Wasu Na Son Sabi’u Tunde Ya Yi Takarar Gwamnan Katsina A 2023

Wasu Na Son Sabi’u Tunde Ya Yi Takarar Gwamnan Katsina A 2023

0

Wasu Na Son Hadimin Shugaban Kasa, Sabi’u Tunde Ya Yi Takarar Gwamnan Katsina A 2023

Yayin da zabukan shekarar 2023 ke ta kara karatowa, harkar siyasar a jihar Katsina tana ta kara yin zafi kulum.

Haka zalika musamman duba da cewar Gwamnan Jihar, Alhaji Aminu Bello Masari zai kammala wa’adin mulkin sa ne a zaben mai zuwa, kujerar ta Gwamna na cikin kujerun da mutane da dama ke hari.

Daman dai Hausawa na cewa kowa da kiwon da ya karbe sa, to wata kila hakan ne ma yasa wasu mutane ke son daya daga cikin hadiman Shugaban kasa kuma matashi, mai suna Sabi’u da ke ma lakabi da ‘Tunde’ ya fito takarar Gwamnan Katsina.

Shi dai Sabi’u Tunde, kamar yadda aka fi sanin sa, yanzu yana daya daga cikin makusantan Shugaban Kasar kuma shine ma mai taimaka masa tare da yi ma mutane iso wurin Shugaban Kasar a ofishin sa.

Jaridar Katsina Post dai ta yi kicibis ne fa fostar sa ta neman takarar Gwamnan a shafukan sadarwar zamani wanda wani mai suna Sule Dudu Kofar Sauri ya dauki nauyi.

Tunde dai yana daga cikin matasa masu karancin shekaru da ake zaton suna da kudi da tarin dukiya a Najeriya.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: