Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Jirgin Yaki Ya Gigita Barayi A Dajin Katsina, Mutane 20 Sun Kubuta
Jirgin Yaki Ya Gigita Barayi A Dajin Katsina, Mutane 20 Sun Kubuta

Jirgin Yaki Ya Gigita Barayi A Dajin Katsina, Mutane 20 Sun Kubuta

0

Jirgin Yaki Ya Gigita Barayi A Dajin Katsina, Mutane 20 Sun Kubuta 

Sojoji Su Kubutar Da Mutane Da Dama A Dajin Rugu Na Jihar Katsina

Mutane 20 Sun Kubuta Bayan Wata 5 A Hannun ‘Yan Bindiga A Dajin Katsina

Wani Jirgin Yakin Sojin Sama na Najeriya ya gigita barayin daji dake fakewa a cikin dajin rugu na Jihar Katsina wanda hakan ya sanya suka ruga domin neman mafaka.

A sabili da wannan gigitawa da Jirgin ya yiwa barayin ya sanya wasu mutane kimanin su 25 da barayin sukayi garkuwa da susun samu hanyar kubuta daga hannun barayin a sa’ilinda suka ara a cikin na kare domin neman mafaka daga harin Jirgin.

Kamar yadda wasu da suka samu nasarar kubuta daga cikin mutanen suka bayyana,barayin sunyi garkuwa da su kimanin watanni 5 da suka gabata Kuma suna tsare da su a cikin daji.

Wadanda suka kubuta din sun hada da mata da Maza gami da kananan yara.

Kamar yadda suka shaidawa majiyarmu ta The Fact 24 wasu daga cikinsu anyi yunkurin Kai kudin fansa domin karbarsu daga hannun barayin,sai dai sun kashe wasu daga cikin masu Kai kudin a Yayinda sauran suka ara a cikin na kare.

Wannan cigaba na kubutar mutanen na zuwa ne a dai-dai lokacinda Jami’an Tsaro ke Kara baza kaimi wajen yakar Yan ta’addan a maboyarsu dake cikin dazuka.

Idan dai ba’a manta ba Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin Jagorancin Gwamna Aminu Masari ta sanya wasu dokoki a jihar dake da manufar shawo kai da Kuma dakile harin masu aikata ayyukan ta’addanci a Jihar.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: