Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Crimes Watch ‘Yan Sanda Sun Chafke Wasu ‘Yan Bindigan Da Sukayi Tuban Mazuru A Katsina
‘Yan Sanda Sun Chafke Wasu ‘Yan Bindigan Da Sukayi Tuban Mazuru A Katsina

‘Yan Sanda Sun Chafke Wasu ‘Yan Bindigan Da Sukayi Tuban Mazuru A Katsina

2

‘Yan Sanda Sun Chafke Wasu ‘Yan Bindigan Da Sukayi Tuban Mazuru A Katsina 

Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar Chafke wani Mai shekaru 43 Mai suna Abdullahi Mai-Rafi dake zaune a Kofar Marusa Low-cost da Abbas Haruna Mai shekaru 34 mazaunin unguwar Filin Polo tare da Usman Mai shekaru 50 Dan Kauyen Ganuwa a Karamar Hukumar Charanchi wadanda dukkansu tubabbin masu aikata laifukan ta’addanci ne Kuma da suke taimakawa Gwamnatin Jiha wajen shawo kan matsalar rashin Tsaro bisa zargin yaudara da aikata sata akan cewa suna aiki ne a Ofishin Mai ba Gwamna Shawara akan Harkokin Tsaro.

Kakakin rundunar Yan Sandan SP Gambo Isah ne ya gabatar da masu laifin da sauran masu aikata laifuka daban-daban.

Kamar Yadda SP Gambo Isah ya bayyana,wadanda ake zargin a ranar 11 ga watan Ogusta na wannan shekarar,sun shiga dajin Danmarke dake Karamar Hukumar Ingawa da mota kirar Toyota Camry Mai lamba DE 631 LED,inda suka samu Alhaji Gide Suleiman Dan asalin Karamar Hukumar Malumfashi a rugarshi da wukake da sanduna inda sukayi gargadi gareshi da yaranshi cewar suna aiki ne a Ofishin Mai Ba Gwamna Shawara akan Harkokin Tsaro Kuma suka ce wani Sa’idu ya sace Shanun Lawal saboda haka ya nemo Lawal din ko ya kawo Shanu 100.

Bayan lokaci ana Magana wadanda ake zargin sun damfari Alhaji Gide Shanu 20 da aka kiyasta cewa sun wuce miliyan 7 da dubu 500 Wanda suka ce wai zasu kaiwa Lawal din da aka sacewa Shanu.

Haka zalika sun chaje Alhaji Giden inda suka masa fashin kudi Naira dubu 40 da wayoyin hannu 4.

Bugu da kari Abdullahi Mai Rafi ya kara niyyar yaudarar Alhaji Gide wasu Shanun 20 inda a nan aka samu nasarar chafkeshi.

Kamar Yadda bincike ya tabbatar wadanda ake zargin sun amsa laifinda ake tuhumarsu Kuma sunce sun sayar da Shanun ne a Kasuwar Dankama.

Comment(2)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: