Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An kama manyan barayin mashina da barayin zaune a Katsina
An kama manyan barayin mashina da barayin zaune a Katsina

An kama manyan barayin mashina da barayin zaune a Katsina

0

An kama barayin mashina da barayin zaune masu saye idan sun sato a Katsina

Rundunar Yansandan Jahar Katsina ta samu nasarar kama wasu manyan barayin babura da kuma masu sayen baburan idan sun sato.

Kakakin Rundunar Yansandan na Jahar Katsina SP Gambo Isah ya gabatar da masu laifin ga Yan Jarida, a madadin Kwamishinan Yansandan Jahar Sanusi Buba, a wani taro daya wakana a Shalkwatar Rundunar dake Katsina.

A yayin taron, SP Gambo Isah ya gabatar da wasu mamatasa da suka kasance manyan barayin Mashina, da suke satar mashinan Mutane a cikin garin Katsina, gami da masu sayen Mashinan da aka cafke.

Wadanda aka kaman sun hada da wani Shamsu Sani mai Shekaru 32 dan Unguwar Yammawa da aka kama da mashin din sata a garin Kankiya.

SP Gambo ya kara da cewa da suka tsananta bincike, sai gashi sun kama wasu mutane biyu da ke siyen mashinan satar da mashina biyar wadanda ake kyautata zaton cewa na sata ne.

Haka zalika jami’an ‘yan sandan sun kama wasu mutane hudu da suka hada da Abdulmalik Haruna, Habibu Kabir, Lawal Magaji da kuma Hassan Usman da wasu mashinan sata guda biyu akan hanyar su ta zuwa Jibia.

Nan ma SP Gambo Isah yace da jami’an su suka tsananta bincike sai gasu sun kamo wasu mutanen biyu a cikin garin Katsina da suka hada da Shamsu Sani da Bishir Ladan da mashina uku duk na sata.

SP Gambo ya kara da cewa yanzu dai suna nan suna cigaba da bincike kafin gurfanar da su gaban kotu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: