Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Lafiya Jari: Illolin cin soyen nama, balangu da kuma tsire masu ban tsoro
Lafiya Jari: Illolin cin soyen nama, balangu da kuma tsire masu ban tsoro

Lafiya Jari: Illolin cin soyen nama, balangu da kuma tsire masu ban tsoro

1

Lafiya Jari: Illolin cin soyen nama, balangu da kuma tsire masu ban tsoro 

Yau ta ke babbar Sallah a kasashe da dama ciki kuwa hadda Najeriya.

Ita dai babbar Sallah ta kebanta ne musamman da layya, inda musulmai kan yanka dabba a matsayin koyi da Annabi Ibrahim.

Saboda layyar da ake yi, wanda mafi yawanci na babbar dabba da ke dauke da jan nama, lokacin ana cin naman sosai.

Sai dai kuma cin jan naman yana da illoli da dama kamar dai yadda za ku karanta a nan kasa:

Sabon bincike na masana ya kara tabbatar da illolin cin jan nama. Sinadarin karfe na iron da jini ke bukata shi ake samu a daya daga cikin amfanin cin nama daga dabbobi.

An shafe shekaru 17 ana binciken, sannan kuma an bi diddigin wadanda ake biciken da rayuwarsu don sanin me suke ci a lokutan abinci.

Jami’ar Amurka ta gudanar da binciken, an kuma sami bayanai da ke nuna cewa cutuka irinsu kansa, kiba, da hawan jini suna kama masu son cin balangu da kashi daya bisa hudu, kuma sun fi saurin mutuwa, fiye da wadanda bassu cin jan naman.

Masu cin nama kamar na kifi da kaji, farin naman, sun fi samun yar tazara da tsawon rayuwa, musamman in sun hada da atisaye da cin kayan ganye da ‘ya’yan itatuwa.

Masana dai sun gano cewa, sinadarin iron da ke jini shi ne jikin mutum yake bukata idan yaci nama, shi kuma ba safai ake samunsa daga itatuwa ba, shi yasa dole ana bukatar nama amma ba da yawa ba.

Haka ma dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa cin jan nama da kuma naman da aka saka sinadarai mai yawa na kara yiwuwar kamuwa da cutar sankara.

Comment(1)

  1. I am baffled that this is coming from you guys. I have great respect for your blog but now I know better than to rely on you. Why should this test and the outcome be conducted by an American institution. Don’t you think this is another grand design to stop the Muslim ummah from observing the rituals of sacrificing Rams and other animals as stipulated in the Qu,ran. My dear abeg look for something to tell us not this nonsense.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: