PROPERTIES FOR SALE IN ABUJA

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

CHERISH COLLEGE OF HEALTH

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

Buy/Exchange Rims and Tyres in Katsina CALL 080-322-22751

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

REPAIR YOUR CAR WINDSCREEN PROFESSIONALLY

Home Gossip Kwartanci: Magidanci ya kama abokin sa tsirara gidan sa a Katsina
Kwartanci: Magidanci ya kama abokin sa tsirara gidan sa a Katsina

Kwartanci: Magidanci ya kama abokin sa tsirara gidan sa a Katsina

1

Magidanci ya kama abokin sa ya je kwartanci gidan sa a Katsina

Kwartanci: Magidanci ya kama abokin sa tsirara gidan sa a Katsina 

Wani magidanci ya kama abokin sa tsirara yaje kwartanci gidan sa a Unguwar Modoji, nan cikin birnin Katsina (mun sakaya sunan su).

Shaidu sun tabbatar ma Katsina Post cewa wanda aka kama din aboki ne na kut-da-kut da wanda aka je ma kwartancin.

Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadin da ta gabata da marece.

Mun samu labarin cewa kwarton ya dade yana neman matar abokin nasa amma ta ki bashi hadin har ma ta kai ga ta fadawa mijin na ta.

Sai dai mijin da farko bai yadda ba saboda ganin irin alakar da ke tsakanin su da abokin na sa har sai daga baya.

“Matar ta dade tana fadawa mijin nata cewar abokin sa yana yi mata maganganun banza har ma yana neman ta.

“Amma shi mijin ya musanta kalaman matar saboda kallon irin alakar abotar da ke tsakanin su”, inji wani abokin mutanen biyu da ya bukaci a sakaya sunan sa.

Abokin ya cigaba da shaidawa Katsina Post cewa “Ranar da dubun kwarton ta cika magidancin ne ya fadawa abokin nasa cewar yayi tafiya amma sai ya labe a cikin ‘ceiling’ sannan ya hada baki da matar sa akan ta kira kwarton kuma ta ja hankalin sa har ya cire kayan jikin sa.

“Hakan kuwa na faruwa sai magidancin ya fito daga maboyar sa sannan ya kuma yi kururuwa abokan sa suka shigo gidan inda suka kama shi tsirara”.

Haka dai suka yi ta bugun kwarton sannan suka lalata mashi mashin din sa roba-roba da ya je kwartancin da shi kafin daga bisani su kai shi a wurin ‘yan sanda.

Allah ya tsare mu daga mummunar kaddara. Amin.

Comment(1)

  1. Wannan kwarto ba ɗan Hambali Family, Unguwar Alkali bane kamar yadda ya ce a bidiyon!
    Shi suruki ne kawai na wani maƙwabcin Unguwar Alkali, kuma abinda yake kawo shi Unguwar mu ke nan.
    BA MU SAN SHI BA!

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Aminchi Klin Motors

%d bloggers like this: