PROPERTIES FOR SALE IN ABUJA

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

CHERISH COLLEGE OF HEALTH

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

Buy/Exchange Rims and Tyres in Katsina CALL 080-322-22751

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

REPAIR YOUR CAR WINDSCREEN PROFESSIONALLY

Home Katsina Post HAUSA Mamakon ruwa da iska ya kashe mutum 1, da rusa gidaje sama da 200 a Katsina
Mamakon ruwa da iska ya kashe mutum 1, da rusa gidaje sama da 200 a Katsina

Mamakon ruwa da iska ya kashe mutum 1, da rusa gidaje sama da 200 a Katsina

0

Mamakon ruwa da iska ya kashe mutum 1, da rusa gidaje sama da 200 a Katsina

Bayan rasa rayuka, sama da gidaje 200 sun rushe saboda mamakon ruwa da iska a Faskari

Abin tausai da jimami ya shafi al’ummar karamar hukumar Faskari, inda gidajen talakawa sama da kusan dari biyu sun rushe bayan rasa rayuka da aka yi.

Ruwan da ya wakana a yammacin ranar jiya Jumu’ah da wajen karfe 6 na yamma, ya yi sanadiyar mutuwar wata karamar yarinya da ta fake jikin wata katanga ta gidan kifi dake yankin dam cikin garin Faskari, inda katangar ta fadi ta danne yarinyar da aka bayyana cewa diyar Gambo Badada ce.

Haka kuma Katsina Daily Post News ta binciko cewa akalla sama da gidaje dari biyu sun tabu sakamakon ruwa da isakar, inda wani gidan ya zube gaba daya, wani rufin dakin ya kekkece, wani kuma katangu da sauran abubuwa masu amfani sun fadi duk sun lalace.

A wani rubutu da Ibrahim M Bawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, game da faruwar ifti’la’in a Faskari, ya yi kira ga mahukunta karamar hukumar da masu hali da su shiga cikin lamarin domin taimakon wadanda abin ya shafa cikin gaggawa.

“Zuwa ga wakilanmu tun daga matakin Sanata har zuwa dan Majalissar jiha dake wakiltar karamar hukumar Faskari, ga wani agajin gaggawa da muke bukata a gare ku.

A yau an yi mamakon ruwa da iska, a cikin garin Faskari da kewaye, wanda a sanadiyar hakan, magidanta da dama sun rasa gidajensu, wasu sun rasa shagunansu, wasu kuma sun sami babban gyara a saman kwanon rufinsu, wasu ballewar katangu, da idan an kiyasta hakan, asarar da aka tabka za ta ci miliyoyin naira.

A rubutun nan da nake rubutawa a yanzun, gidan makwabcina (Abdulganiyu Ruguji) ya rushe kaf, bayan yakicewar rufin dakunan gidan, in ka shiga cikin gari da sauran unguwannin dake gefen gari, abun ba dadin gani, wani za ka tarar da katangunsa sun fadi, wani kwanon rufinsa ya kife, ba a maganar falwayoyin lantarki da itatuwan cikin gidaje da kofar gidan mutane.

Abin tausai a nan shi ne yadda al’ummar ke cikin halin rashi, ga kuma wannan iftala’in, muna kira a gare ku tun daga kan sanatanmu Distinguish Bello Mandiya, da wakilinmu a Majalissar wakilai Hon Murtala Isah Kankara, da kuma dan Majalissarmu na jihar Katsina Hon Engr. Shehu Dalhatu Tafoki, da su shigo su saka kwamiti a samar wa al’ummarmu gudunmuwar gyaran gidajensu tun daga matakin Tarayya har zuwa na jiha.

Ba ma su kadai ba da alhakin hakan ya ta’allka a wuyansu zuwa ga gwamnati, har da ma duk wani mai hali da muke da su a karamar hukumar Faskari,ga wata hanyar samun lada da taimakon jin kai.

Wallahi abin ba dadi, akwai ban tausai , yadda za ka ga magidanci na fama da abin da zai ci, ga shi kuma ya gamu da irin wannan ifti’la’i.” Ibrahim M Bawa

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Aminchi Klin Motors

%d bloggers like this: