PROPERTIES FOR SALE IN ABUJA

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

CHERISH COLLEGE OF HEALTH

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

Buy/Exchange Rims and Tyres in Katsina CALL 080-322-22751

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

REPAIR YOUR CAR WINDSCREEN PROFESSIONALLY

Home Katsina Post HAUSA Tunawa Da Alhaji Dr. Mamman Shata, Shekaru 22 Bayan Rasuwar Sa
Tunawa Da Alhaji Dr. Mamman Shata, Shekaru 22 Bayan Rasuwar Sa

Tunawa Da Alhaji Dr. Mamman Shata, Shekaru 22 Bayan Rasuwar Sa

0

Rana Mai Kamar Ta Yau: Yau Alhaji Dr. Mamman Shata Ya Cika Shekara 22 Cif Da Rasuwa (1999-2021)

Ba Rabo Da Gwani Ba: Tunawa Da Alhaji Dr. Mamman Shata, Shekaru 22 Bayan Rasuwar Sa 

Daga Hamisu Adamu Gamarali Funtua

A rana Mai Kamar ta yau wato ranar 18/06/99 ne Allah SWT ya dauki ran Alh Dr Mamman Shata wani shahararren mawaki da ya shafe sama da shekaru sittin Yana rera wakoki a fage daban-daban da ya shafi rayuwar al’umma.
Zanso inyi amfani da wannan dama don yimashi addua tare da fatan Allah ya gafarta mashi dukkanin kurakuranshi kuma yayi mashi masauki a gidan aljannah.

WASU MAHIMMAN BAYANAI 22 DANGANE DA SHATA

1. Shata ya rasu ranar Juma’a 18/06/99 a asibitin Malam Aminu Kano da misalin karfe 11:30pm

2. Shata ya rasu yana da shekaru 76 a duniya.

3. Shata bai bar wasiyyar a rufeshi a garin Daura ba, kusanci da soyayya dake tsakaninsu da Marigayi Sarkin Daura Muhamnadu Bashar tasa diyarshi Barr Jamila Shata wadda ita ce ke tare dashi lokacin da ya rasu to dauke shi ta kaishi Daura kuma akai mashi sutura a can.

4. Shata ya rasu ya bar matan aure ukku:

1. Hajia Furera (Ta rasu)

2. Hajiya Hadiza (Ta Falgore)

3. Hajiya Amina (Ta Dukke)

5. Haka Kuma Shata ya bar y’ay’a 20 guda 9 maza guda 11 mata:

1. Lawal Shata (Magaji)

2.Mamuda Shata (ya rasu 2017)

3. Aminu Shata

4. Salisu Shata

5. Nura Shata (ya rasu 2016)

6. Sagir Shata (Bala)

7. Bishir Shata

8. Muntari Shata

9. Sunusi Shata (Khalifa)

10. Binta Shata (Mami)

11. Hadiza Shata

12. Amina Shata

13. Barr Jamila Shata

14. Bilkisu Shata

15. Hadiza Shata (Lami) ta rasu 2003

16. Hauwa Shata

17. Halima Shata

18. Ramatu Shata

19. Umma Shata

20. Rabi Shata

6. Shata ya mallaki motar hawa ta farko tun shekara ta 1953

7. Shata sau daya rak ya je aikin Hajji wato a shekara ta 1956. Sai dai ya biyawa mutane da dama sunje makka. Ko a shekara ta 1970 ya biyawa mutum 20 suka tafi lokaci daya.

8. Shata ya kai Kassu Zurmi da Sale Gambara da Muhammadu Gawo Filinge da “Kusoshin birni Uwawu” Makka.

9. Shata bashi da wasu aljanu a matsayin yan’amshin sama.

10. Shata baya atisayen wak’a, wato (rehearsal)

11. Asalin kakannin Shata Fulani ne daga Sayyina karamar hukumar Tambuwal ta jahar Sokoto.

12. Shata ya taba zama Kansila a karanar hukumar Kankia (lokacin Musawa na karkashi Kankia)

13. Shata ya taba zama SDP Chairman Party na karamar hukumar Funtua.

14. Shata ya taba bayyana aniyar tsayawa takarar shugabancin Nigeria a shekara ta 1992/93 a karkashin jamiyyar SDP.

15. Shata yaje kasar Amurka da London a shakara ta 1989

16 . Mati Attah (D’an-yarbayye) Yana d’aya daga cikin amintattaun yaran Shata Kuma tare dashi akaje America. Duk abubuwan da Shata ya fadi dangane da Mati a wak’a yayi ne cikin wasa da raha.

17. Shata ya samu Digirin digirgir na girmamawa wato (Dr) Wanda ABU ta bashi a ranar 23/01/1988

18. Shata ya samu lambar yabo ta kasa MON (Member of the order of the Niger) a lokacin gwamnatin Obasanjo a ranar 14/03/77

19. Shata ya samu lambar yabo daga shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan a ranar Jumma’a 28/02/ 2014 (Centinary Award)

20. Sardaunan Dutse Alh Bello Maitama shine Wanda Shata yafi yima wakoki da yawa.

21. Shata ne ya fara baiwa Dankabo mota tun lokacin Dankabo na buga bulon sayarwa a bakin hanya.

22. Shata baya cewa “Ya wane” a cikin waka sai dai yace “Wo wane” duk inda kaji yace “Ya” to suman Allah zai kira saboda girmamawa.

Allah ya jikan na Ali hukumar wak’a ya gafarta mashi kuma ya albarkaci zuriarshi baki daya ameen.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Aminchi Klin Motors

%d bloggers like this: