PROPERTIES FOR SALE IN ABUJA

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

CHERISH COLLEGE OF HEALTH

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

Buy/Exchange Rims and Tyres in Katsina CALL 080-322-22751

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

REPAIR YOUR CAR WINDSCREEN PROFESSIONALLY

Home Katsina Post HAUSA Umar Tata ya bayyana kudurin sa na takara a zaben 2023

Umar Tata ya bayyana kudurin sa na takara a zaben 2023

0

Umar Tata ya bayyana kudurin sa na takara a zaben 2023

Zan nemi takarar Gwamna a shekarar 2023 – Inji Umar Tata 

Daga Suleiman Umar

Dan siyasar nan da sha takarar neman gwamna a baya Alhaji umar Tata ya bayyana ma jaridun katsina city news cewa ya fito a tsanake da kuma shirin shi don neman takarar gwamnan katsina a zaben 2023 mai zuwa in Allah ya kaimu.

A wata tattaunawa da babban editan jaridun yayi dashi ta waya daren talata 8/6/2021.Alhaji Umar Tata ya bayyana cewa ya bada takardar sa ta sanarwar kudurinsa na ajiye aiki a inda ya koma aiki a gwamnatin tarayya.

Kuma yanzu ya komo harkar siyasa da neman takarar gwamnan katsina gadan gadan a shekarar 2023 insha Allah.

Da aka tambaye shi wane matsayi yanzu yake a neman takarar tasa? Yace yanzu muna matakin ganawa da mutane da magana da dattawa da kuma duk wani abu da bai Saba ma dokar zabe ba.ko neman takara.

Yace wasu motoci da aka ga suna yawo a duk fadin jahar katsina, da yawan su masoyanshi ne.da wadansu da ya taba taimako yanzu suna da hali suke saye suna badawa a matsayin gudummuwa.

Umar Tata yace a wata mai kamawa zai wani shirin ganawa da jikokinshi na shiyyar Daura ,katsina, da funtua.

Yace ya ya na matan da ya taba aurar wa a lokacin da ya taba yin wani shiri aurar da Mata a shekarar 2015.

Yace zai gana da ya yan da aka Haifa karkashin wancan shirin kuma zai masu Alheri abin da Allah ya hore.

Umar Tata yace zai fito takarar shi ne a karkashin jam iyyar sa ta APC.

A baya Tata ya taba neman takarar gwamnan katsina a karkashin jam iyyar PDP da kuma jam iyyar APGA. yanzu kuma ya kuduri niyyar fitowa a jam iyyar APC a zaben 2023.

Mun kalato daga Katsina City News

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Aminchi Klin Motors

%d bloggers like this: