Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An kama likitan ‘yan bindiga a Katsina
An kama likitan ‘yan bindiga a Katsina

An kama likitan ‘yan bindiga a Katsina

0

An kama likitan ‘yan bindiga a Katsina

Rundunar yan sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar cafke wani wanda ake zargi da zama likitan’ yan bindiga a dajin Katsina.

Kakakin rundunar yan sandan na jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya gabatar da wanda ake zargin gaban yan jarida a ranar Litinin.

Wanda ake zargin dai mai suna Murtala Umar, mai shekara 34 ya ce yayi karatun lafiya sa ne a wata makarantar koyon aikin lafiya dake nan jihar Katsina.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, Murtala ya amsa cewa yana zaune ne a garin Tashar Yan Alewa dake a Karamar hukumar Danmusa kuma yana da shagon shan mangani watau ‘Kemis’.

Haka ma dai Murtala ya ce ‘yan bindigan kan zo da bindigu su tsare shi sai ya yi masu allura ko ya ba su magani ko kuma suyi barazanar kashe shi.

Amma da kakakin rundunar yan sandan ya tambaye shi ko ya sanar da mahukunta irin barazanar da yake fuskanta sai yace a’a.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: