Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Latest Mustapha Inuwa da Mahdi Shehu: Yadda zaman kotu ya gudana a yau
Mustapha Inuwa da Mahdi Shehu: Yadda zaman kotu ya gudana a yau

Mustapha Inuwa da Mahdi Shehu: Yadda zaman kotu ya gudana a yau

0

Mustapha Inuwa da Mahdi Shehu: Yadda zaman kotu ya gudana a yau 

Bayan Alkalai (Maishari’a Abbas Bawale da Maishari’a Muhd Ashiru Sani sun zauna, an kira karar da Mahadi Shehu ya daukaka domin ci gaba daga inda aka kwana.

Lauyan Mahadi Shehu, Barista Abbas Machika ya mike inda ya sheda ma Kotu cewa a ranar 5 ga watan jiya sun shigar da wata takarda ta neman a ba su dama su shigar da kari akan dalilansu na daukaka kara.

Yayin da Kotu ta waiwayi Lauyan Sakataren Gwamnatin Jihar Mustapha Muhammad Inuwa, Barista Abubakar Sahu Ibrahim ya ce ya amince da a ba su dama.

Anan ne Lauya Abbas Machika ya sheda mu Kotun cewa sun shirya don gabatar da dalilan su guda shida.

Shi ma kuma Lauya Abubakar Ibrahim ya ce a shirye ya ke, a ci gaba da fafatawa.

Ganin cewa sauraren su zai dauki dogon lokaci sai kotu ta ce a ba ta dama ta sallami kararrakin da ba za su dauki dogon lokaci ba.

A haka aka fita har sai da misalin 3:40pm aka dawo cikin Kotun sa’annan aka ba Lauyan Mahadi dama ya soma gabatar da koken su.

Ya soma da cewa dalilansu na daga kara guda shida ne wadanda akan su zai nemi kotu ba su amsa.

Abu na farko, ya ce shi ne cewa tun farko an shigar da kara ta laifi (criminal) ka tsaye akan Mahadi Shehu a karkashin wata doka ta 188 ta kundin tsarin Shari’ar Musulunci ta Jihar Katsina.

Ya akan wannan ne Kotun baya ta tuhumi Mahadi, har ta kai ga ta ba shi sammaci kuma ta ba da umurnin a kamo shi.

Ya ce sai dai kuma kundin tsarin waccan doka ya baiwa Majalissar Dokoki ta jiha dama na ta yi kundin tsarin laifuffuka da hukuncinsa wanda da shi ne kadai za a iya aiwatar da shari’a a karkashin wancan sashe na 188.

Abbas Machika ya ce har yanzu Majalissar Dokokin ba ta yi wannan aikin ba, saboda haka cajin da aka yi ma Mahadi a karkashi wannan doka ya keta yancinsa na dan adam kuma ba a yi masa adalci ba.

Ya kawo misalai na wasu shari’u da hukunce-hukuncen Kotun Koli ta Nijeriya wadanda a cewar sa duk suna nuni da cewa rashin wancan kundin tsarin laifuffuka da hukuncin su ya bata duk wata shari’a da aka yi ma wani karkashin waccan doka.

Na biyu, Barista Machika ya bukaci Alkalan da su duba wasu shafuka na kwafen takardun shari’ar da waccan Kotun ta yi inda ya ce Alkalin waccan Kotun ya jingine rokon lauyan mai kara, kana ya hukunta cewa wajibi ne wanda ake kara ya gurfana a gaban sa.

Akan wannan ma Lauyan ya kafa hujja da wani hukuncin Kotun Koli wanda a cewar sa akan yi watsi da duk wata tuhuma da aka yi ma wani muddin babu Kundin tsarin laifuffuka da hukuncin su.

Daga karshe ya ce haka kurum bayan kwanaki 6 da sauraren shari’a Alkalin Kotun ya bada umurni a kamo wanda yake tsaya mawa alhali ya kuma ba da kwanaki 14 ga duk mai sha’awar daukaka kara.

Anan ma ya ce Kotun Daukaka Kara ta hukunta cewa muddin ana kalubalantar inganci ko hurumin kotu kuma wanda ake tuhuma ya daukaka kara kafin akai ga gurfanar da shi a gaban Kotu kamar yadda wanda yake karewar ya yi.

Daga karshe Lauya Machika ya roki Kotun da karbi rokonsu na neman a soke shari’ar da waccan Kotun ta baya ta gudanar.

Bayan da ya zauna sai kotu ta baiwa Lauyan Mustapha Inuwa dama ya gabatar da tasa muhawara akan batutuwan da Lauyan Mahadi ya yi.

Barista Abubakar ya fara da batu na farko yana mai cewa cajin da ake yi wa wanda ake tuhuma ba ya faduwa don kawai an caje shi a karkashin wata doka wadda ba ta aiki.

Ya kafa hujja da wani hukuncin Kotun Koli ta Nijeriya inda ta hukunta cewa cajin da aka shigar a cikin sammacin da takardar sa na dauke da lambar dokar da ba ta aiki na zama daram muddin:

(i) Cajin da ake yi ma wanda ake kara laifi ne a karkashin wata doka wacce ke aiki.

(i) Kotun da aka shigar da karar tana da hurumin sauraren shari’ar.

Ya ce anan tuhumar da ake yi ma Mahadi ta bata suna ce, kuma akwai doka mai ci yanzu mai suna Kundin Tsarin Shari’ar Musulunci ta Jihar Katsina.

Haka kuma Kotun Shari’ar da aka kai Mahadi tana da cikakken hurumi na sauraren kara ta laifi ba tare da la’akari da wace lambar doka aka yi amfani da ita wajen rubuta sammaci.

Barista Abubakar ya yi ta ruwan misalai daga hukunce-hukuncen Kotun Koli da na Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da kuma hujja daga ayar Alkur’ani Maigirma wadda ta umurci Alkalai da su yi adalci akan abinda duk ya bayyana na gaskiya a gaban su akan Attajiri ko Matalauci, Maimulki ko Talaka ba tare da jin tsoron abinda zai faru ba.

Dangane da batun rashin wani kundin tsarin laifuffuka da hukuncin sa na Shari’a wanda Lauyan Mahadi ya kawo cewa Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina ba ta yi shi ba, Lauyan Mustapha Inuwa ya ce babu inda suka yi wannan magana a gaban waccan Kotun ta baya. Yana mai cewa sai a wannan Kotun ce suka shigo da batun ba tare da neman izinin ta ba. Bugu da kari ya ce ita ko daukaka kara ana yin ta ne kadai akan gundarin abinda ya gudana a gaban karamar Kotun da aka fito.

Akan koken da Lauyan Mahadi ya yi na cewa Kotun baya ta keta yancin Mahadi, ba ta ba shi dama ya kare kansa ba, ya ce ko alama ba bu inda Kotun shari’ar Musulunci ta tauye masa hakki.

Dalili shi ne ai ba a ma fara sauraren shari’ar Mustapha Inuwa da Mahadi ba, saboda tun ranar da aka shigar da karar, Mahadi bai taba zuwa Kotun ba, ballantana ma ace an yi masa rashin adalci ko tauye haki.

Ya kawo misalin hukuncin Kotun Koli wadda ta ce Shari’a na farawa ne daga lokacin da aka gurfanar da wanda ake tuhuma, aka karanta masa cajin da ake yi masa kuma aka tambaye shi ya ji, ya aikata ko bai aikata ba?

Ya hakikance da cewa babu inda hakan ya afku a gaban Kotun shari’ar tun da Kotun har yanzu ba ta taba sanya shi a ido ba.

Dangane da batun daga Shari’a zuwa kwana 6 kafin kwanaki 14 na daukaka kara da Alkali ya bada bai tauye hakin kowa ba saboda Alkali ne kadai ke da ikon daga kara zuwa ranar da ya ga dama.

Ya kawo misalin shari’u da dama inda ya tabbatar da hakan. Ya ma buga hujja daga cikin wani Littafin Fassarar “Tuhfatul Hukam” wanda shi Lauyan Mahadin Abbas Machika da kansa ya wallafa, inda yake tabbatar da cewa Alkali ke da cikakken ikon daga kara.

Lauya Abubakar ya kuma soki koken da Lauyan Mahadi ya yi akan umurnin da Alkalin Kotun Shari’a ya bada cewa a kamo shi.

Ya ce ai yin hakan ya zama wajibi saboda hurumin Alkali ne ya hukunta duk wanda ya rena Kotu.

Ya ce, a bayyane take Kotu ta umurci Mahadi ya bayyana a gabanta ta hanyar Lauyan nasa, amma aka wayi gari; shi bai zo ba, Lauyansa bai zo ba kuma ba kuma babu wani sako da ya zo ma kotu cewa ga dalilin da ya hana su zuwa.

Saboda haka a karshe ya roki Kotun da ta amince da dukkan hujjojin da ya gabatar ta yi watsi da korafe-korafen Mahadi da Lauyan shi.

Sai dai shi ma Lauya Macika ya roki Kotun da kara ba shi dama ya mayar da martani akan wasu batuwa sabbi da ya ce Lauyan Mustapha Inuwa ya zo da su.

Akan haka Maishari’a Abbas Bawale ya daga zuwa gobe Talata 28 ga wata da 9:00am don sauraren martanin da Barista Abbas Machika zai mayar.

An tashi zaman Kotun da karfe 6:10pm.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: