Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Wata kungiya ta raba Zakkar Naira miliyan 4 a Katsina
Wata kungiya ta raba Zakkar Naira miliyan 4 a Katsina

Wata kungiya ta raba Zakkar Naira miliyan 4 a Katsina

1

Wata kungiya ta raba Zakkar Naira miliyan 4 a Katsina 

Wata kungiya wadda ba ta Gwamnati ba mai rajin cigaba jihar Katsina watau Home of Hospitality Development Initiative, HOHDI a turance dake a jihar Katsina ta jagoranci rabon zakka ta Naira miliyan hudu ga mabukata a jihar.

Kudin Zakkar dai wani Kamfani new dake hada-Hadar kudade mai suna APT Securities And Fund Limited ya bayar da su.

Kimanin mutane 200 ne Kuma suka anfana da Zakkar inda kowa ya samu Naira dubu ashirin ashirin.

Taron rabon Zakkar dai wanda ya gudana a dakin taro na tsohon gidan Gwamnati yanzu samu halartar shugabannin kungiyar HOHDI din da kuma na kamfanin APT da ma shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya na SMEDAN da NDE.

Da yake gabatar da lacca a wurin taron kafin a fara rabon kudin, Shugaban hukumar SMEDAN a jihar Katsina, Alhaji Abdulkadir Tsanni ya ja hankalin wadanda suka ci gajiyar Zakkar da su fidda wani dan kaso daga cikin kudin su fara sana’a domin dogaro da kai.

Shima Shugaban hukumar Samar da ayyukan yi ta kasa watau NDE, Alhaji Yarima ya tunasar da wadanda suka anfana da zakkar irin albarka da alfanun da ke cikin sana’a komin kankantar ta sannan ya shawarce su da su tattala kudin kada su je su banzatar da su wajen abubuwan da ba muhimmai ba.

Tun farko da yake jawabin maraba a wurin taron, wani jami’in kungiyar, Dr Bashir Kurfi ya bayyana cewa sun zakulo mutanen da za su anfana da shirin ne bisa la’akari da bukatar su.

Daya daga cikin wadanda suka anfana da tallafin Malama Binta Haruna daga karamar Funtua da yi jawabi a madadin sauran ta godema kungiyar da ta shirya shirin da kuma kamfanin da ya fitar da zakkar tare kuma da yin addu’a Allah ya kara daukaka su.

Daga karshen taron dai an rabawa mutanen da aka zakulo zakkar karkashin jagorancin Shugaban shiyya na kamfanin APT Securities and Funds Limited, Alhaji Sagir Ubaidu.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: