Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Kafi-Mai-Kafa-Lalata: An kama gurgu gawurtaccen dan ‘ta’adda a Katsina
Kafi-Mai-Kafa-Lalata: An kama gurgu gawurtaccen dan ‘ta’adda a Katsina

Kafi-Mai-Kafa-Lalata: An kama gurgu gawurtaccen dan ‘ta’adda a Katsina

1

Kafi-Mai-Kafa-Lalata: An kama gurgu gawurtaccen dan ‘ta’adda a Katsina 

Dubun wani mai buƙata ta musamman ta cika a ranar 18/9/2021 inda jami’an tsaro suka damƙe wani matashi mai suna Buhari Haruna, dan kimanin shekaru 22 daga ƙaramar hukumar Kankia.

Mai magana da yawun Rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da shi tare da sauran masu laifin ga ‘yan jarida a ofishin su.

A cewar Gambo Isah, matashin ya ƙware ne wajen kiran wayar Salular Mutane yayi masu barazanar cewa su bashi kuɗin fansa ko kuma za’a sace su ko wasu makusantansu.

Rana ta baci a gare shi yayin da ya kirawo wani dan kasuwa mai suna Hamisu Saminu, dake ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina ya buƙaci da a biya shi kuɗi har Naira Milyan Biyu (2, 000, 000:00K) a matsayin kuɗin fansa ko kuma a sace shi ko wani na kusa da shi.

Jami’an tsaro sunyi nasarar chafke wanda ake zargin yayin da yazo karɓar wani kaso na kuɗin fansar da akayi dashi yazo ya karɓa a wani wurin da ya bada da kanshi.

SP Gambo Isah yace rundunar na cigaba da binciken lamarin kuma da zarar an kammala za su gurfanar da shi gaban kuliya.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: