Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Tarihi Garuruwa Tarihin Garin Bindawa, ta Dan Bindi da Bindau Mai Abun Mamaki
Tarihin Garin Bindawa, ta Dan Bindi da Bindau Mai Abun Mamaki

Tarihin Garin Bindawa, ta Dan Bindi da Bindau Mai Abun Mamaki

0

Tarihin Garin Bindawa, ta Dan Bindi da Bindau Mai Abun Mamaki 

– Garin Malamai Da ‘Yan Boko 

– Bindawa ta Dan Bindi da Bindau Mai Abun Mamaki 

– Kabari Mai Kayan Gani Daga Nesa 

– Garin Bani-Bani Ba Mai Baka, Sai Dai Ka Tashi Ka Nemi Na Kan Ka

Wasu habe ne wadanda suka taso daga wani ƙauyen da ake kira rugar Jibir su suka kafa Garin BINDAWA a cikin shekara ta 1770.

Asalin sunan BINDAWA ya samu ne daga wani mutum Mai suna Bindau wanda akayi a lokacin Sarakunan Habe. Tarihi ya nuna cewa da Bindau ya rasu sai aka rufe shi a Rigar Jibir kusa da Damakwaro.

Daga baya sai mutanen Rigar Jibir suka tashi suka bar Garin, suka tafi dai dai inda Bindawa take suka kafa sabon Garin su. Daga nan sai aka riƙa kiran wurin da suna Bindawa, watau mutanen da suka taso daga Rugar Jibir inda aka rife Bindau.

Game da sha’anin mulki, Tarihi ya nuna cewa wani Malami Mai suna Yusuf, shine ya fara Sarautar Dagaci a Garin BINDAWA, a lokacin Sarakunan Habe wajen shekarar 1770. Bayan ya rasu Kuma aka nada dansa Mai suna Dan Yusufa, Kuma da haka ake Kiran Sarakunan Bindawa tun daga Habe har zuwa FULANI.

A lokacin mulkin FULANI Ummarun Dallaje ya nada wani da ake Kira Bagime Dagacin Bindawa. Bayan rasuwar sa aka nada Addi. Daga shi Kuma sai Abu Dan Ummarun Dallaje. Bayan shi Kuma aka nada Abu. Daga shi Kuma sai aka nada Ahmadu Dan Ummarun Dallaje.

Bayan Dan Bindi Ahmadu Kuma, sai Sarkin Katsina Muhammadu Bello ya nada Danbi di Dibga. Daga shi Kuma aka nada Danbindi Bawa Dan Bebeji Gidado Jikan Ummarun Dallaje. Daga shi Kuma sai Dan Bindi Isah. Sai Dan bindi Bawa. Sai Dan Bindi Ibrahim wato Wanda ya taba yin Sarautar Kankia da Kandawa daga ƙarshe yayi Sarkin Katsina.

Daga shi Kuma sai Sarkin Katsina Abubakar ya nada Danbindi Yakubu. Sai Dan Bindi Aliyu Dan Musa Wanda Sarkin Katsina Yero ya nada. Bayan rasuwar Dan Bindi Aliyu sai aka nada dansa Lawal ya gaje shi. Shi Kuma En’ E ta Katsina ce ta fitar da shi a shekarar 1960, saboda wani laifi daya aikata.

Kuma daga wannan lokacin ne aka canza Sarautar Bindawa daga Dan Bindi ta Koma Magajin Gari. A lokacin ne Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo ya nada Malam Dan Ladi ya Zama Magajin Garin BINDAWA. Shi Kuma Malam Dan Ladi Dan Hakimin Bindawa Dan Yusufa Shehu Usman ne.

A bangaren Hakimi kuwa, Wanda aka fara nadawa Hakimin Bindawa a zamanin mulkin FULANI shine Dan Agga. Bayan rasuwarsa Kuma sai dansa Shagero ya gaje shi a shekara ta 1846. Bayan sa kuma sai aka nada Dan Yusufa Jabba Dan Ummarun Dallaje a shekara ta 1856. Sai Dan Yusufa Ahmadu Dan kyau Dan Ummarun Dallaje Wanda aka nada a shekara ta 1860. Daga shi Kuma sai Dan Yusufa Zaki Dan Shagero Wanda Sarkin Katsina Ibrahim ya nada a shekara ta 1868. Daga shi Kuma sai Dan Yusufa Abu Dan Ummarun Dallaje Wanda aka nada a shekara ta 1872 Kuma yayi kwana tamanin ne bisa gadon Sarauta ya rasu.

Daga shi Kuma sai aka nada Dan Yusufa Isah wato Wanda ya taba yin Sarautar Dagacin ta Dan binbidi a Bindawa. Sai Kuma Dan Yusufa Yahaya Dan Ibrahim Wanda aka nada a shekara ta 1887.

Bayan shi Kuma sai Dan Yusufa Maza Waje Dan Jabba Wanda Sarkin Katsina Abubakar ya nada a shekara ta 1904. Daga shi Kuma sai Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya nada Dan Yusufa Bello Dan Jabba a shekara ta 1919. A cikin wannan lokacin ne Garin Bindawa ya fara bunkasa sosai ta fuskar Ci gaban zamani don kuwa a lokacin ne aka Gina Barikin Bindawa tare da babbar Makarantar Firamare wadda aka bude a shekara ta 1928.

Bayan rasuwarsa Dan Yusufa Bello, sai aka nada dansa Usman Bello a shekara ta 1937. Kafin kuwa yazo ga wannan matsayin sai da yayi Sarautar Kamri. Bayan rasuwarsa sai Dan shi Bello Dangoggo ya gaje shi Wanda Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo ya nada a shekara ta 1965.

Mutanen Bindawa kuwa sun shahara sosai ta fuskar neman ilimi. Wannan irin baiwa da Allah yayi masu ba Karamar Martaba ce a garesu dama Kasar Katsina baki daya ba. A duk faɗin Kasar Hausa da zaa leka idan baka samu Malaman addini Yan asalin Bindawa ba to ka samu gogaggun Yan Boko, Maiakatan Gwamnati. Haka Kuma a fannin Kasuwanci irin na zamani da sanaoin Gargajiya har kwanan gobe akwai masu yin su birjik a Bindawa.

An ƙirkiro ƙaramar Hukumar Bindawa daga cikin ƙaramar Hukumar Mani. Garin Bindawa shine Headquarter ƙaramar Hukumar Bindawa, wadda ta kun shi ƙasar Doro da Bindawa.

Reference.

Garuruwan Jihar Katsina na daya na Hukumar binciken Tarihi da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina page 20-24.

Alhaji Musa Gambo Kofar Soro.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: