Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Rikicin jam’iyyar PDP a Katsina ya kara ta’azzara
Rikicin jam’iyyar PDP a Katsina ya kara ta’azzara

Rikicin jam’iyyar PDP a Katsina ya kara ta’azzara

1

Rikicin PDP a Katsina ya kara ta’azzara

Rikici na cigaba da ruruwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar Katsina sakamakon rashin jituwa da tsarin yadda aka gudanar da zaben kwangires na jam’iyyar a shekarar 2020 da wasu’ yan jam’iyyar suka yi.

Yanzu haka dai jam’iyyar ta PDP ta kasu kashi biyu ne bayan da wani bangare na magoya bayan jam’iyyar suka kafa tasu jam’iyyar mai suna ‘PDP A Gyara’.

Ya’yan jam’iyyar bangaren PDP A Gyara, a ranar Asabar suka gudanar da taron manema labarai biyo bayan matsayar da shugabannin jam’iyyar suka dauka na fatali da tsarin sasancin da bangarorin biyu suka fara yi a baya.

A yayin taron manema labaran da Yan PDP A Gyara suka yi a Katsina, karkashin jagorancin tsohon Sakataren din-din-din na ma’aikatar kananan hukumomi, Alhaji Lawal Rufa’i Safana, sun bayyana rashin gamsuwar su akan yadda suka ce ana gudanar da mulkin jam’iyyar a jihar.

Sun bayyana cewa sun lura akwai rashin yadda da salon yaudara a tsakanin shugabannin jam’iyyar da kuma tsakanin shugabannin da kuma mabiyan su wanda suka ce hakan ba dai-dai bane.

Daga karshe sun kuma bayyana cewa ba su da wani zabi wanda ya wuce su cigaba da shari’o’in da suka shigar a gaban kotu tare da gargadin shugabannin jam’iyyar da cewar hakan ba zai haifar masu da da mai ido ba.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: