Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Gwamna Masari ya inganta albashi da kwazon yan’ kwallon jihar Katsina
Gwamna Masari ya inganta albashi da kwazon yan’ kwallon jihar Katsina

Gwamna Masari ya inganta albashi da kwazon yan’ kwallon jihar Katsina

0

Daidaita Tsarin Biyan Hakkokin Yan Wasa Ya Inganta Kwazon Yan Kwallon Katsina United – Inji Kwamishina Danlami.

Kwamishinan Wasanni Da Cigaban Al’umma na Jihar Katsina Alhaji Sani Aliyu Danlami,yace inganta tsarin biyan hakkokin yan kwallon Katsina United da Gwamna Aminu Bello Masari yayi ya inganta kwazonsu a Gasar Kwararru Ta Kasa da aka kammala.

Alhaji Sani Aliyu Danlami na magana ne a lokacin kaddamar da Mambobin Hukumar Gudanarwar Hukumar Kula Da Harkokin Wasanni ta Jihar Katsina da kuma na Hukumar Bada Agajin Gaugawa ta Jiha SEMA.

Kamar yadda Danlami ya bayyana Kungiyar ta Katsina United saida ta kai siradin tafiya matakin ayi waje da ita a gasar wato “Relegation” to amma da taimakon Gwamna Masari sun tsallake siradin kuma sun gama gasar a mataki na 12.

Alhaji Sani Aliyu Danlami Wanda kuma shine Garkuwan Arewa na 1,Kuma Shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar Bada Agajin Gaugawa ta jiha,yace yan kwallon na Katsina United suna karbar albashi tare da ma’aikatan jiha sabanin wasu jihohi da sai an Kai ruwa rana wurin biyan hakkokin yan wasan Jihar.

Ya kuma yabawa dukkannin masu ruwa da tsaki akan yadda suke jajircewa ta fuskar ganin jiharnan ta samu nasarori a Wasanni daban-daban da Jihar ta Shiga.

Daga nan sai ya hori Mambobin Hukumar Gudanarwarakan suyi aiki tukuru wurin sauke nauyinda aka dora masu tare da bada tabbacin basu goyon bayanda ya dace domin cimma manufar kafa su.

A nashi jawabin a madadin wadanda aka kaddamar,Shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar Kula Da Harkokin Wasanni Kuma Danburan Daura Alhaji Muhammad Daha Umar Farouk ya yabawa Gwamna Aminu Bello Masari akan wannan dama da aka basu.

Alhaji Muhammad Daha ya lashi takobin cewa zasu yi aiki tukuru wurin sauke nauyinda aka dora masu tare da rokon goyon bayan Kwamishinan ta wannan fuska.

Ya kuma maganta akan namijin Kokarin Kwamishinan akan sauke nauyinda yake kanshi,sai yayi mashi addu’ar samun jagorancin Allah SWT wurin sauke nauyin.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: