Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An kama kasurgumin barawon mutane da mai safarar muggan kwayoyi a Katsina
An kama kasurgumin barawon mutane da mai safarar muggan kwayoyi a Katsina

An kama kasurgumin barawon mutane da mai safarar muggan kwayoyi a Katsina

0

An kama kasurgumin barawon mutane da mai safarar muggan kwayoyi a Katsina 

Rundunar Hukumar Kula Da Lafiyar Yan Kasa ta Jihar Katsina NSCDC,ta samu nasarar chafke wani mai suna Abubakar Sani dan asalin Kauyen Mai Kaho mai kimanin Shekaru 20 da haihuwa da ake zargi da aikata laifukan satar shanu da garkuwa da mutane, kamar yadda The Fact 24 ta ruwaito.

Kakakin Rundunar DSC Muhammad Tukur Abdara ne ya gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Hedikwatar Rundunar dake Katsina.

Kamar yadda DSC Abdara ya bayyana,Wanda ake zargin Jami’an Sintiri ne suka damkashi ga Jami’an Hukumar a lokacinda suka samu nasarar damkeshi.

DSC Abdara yace wanda ake zargin ya amsa laifin cewa yana cikin kungiyar wasu mutane su 5 da suke aikata laifukan ta’addanci ta hanyar yin amfani da bindigar AK 47 inda suka taba Kai hari a kauyen Nasarawar Bugaje.

Wanda ake zargin ya Kuma amsa shiga a cikin wani laifin garkuwa da mutane 3 da akayi a Kauyen Falale Wanda basu samu nasara ba sakamakon sanar da Jami’an Tsaro da al’umar yankin suka yi.

Kakakin Rundunar yace da zaran an kammala bincike za’a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Bugu da kari Rundunar ta NSCDC ta Jihar Katsina ta kame wani Mai suna Aminu Mu’azu dan asalin Kauyen Yangora ta Karamar Hukumar Bindawa da ake zargi da sayar da kayan maye.

Kayayyakinda aka kame a hannun Wanda ake zargin sun hada da kati 3 na kwayar Diazapham sai Robe 27 na tabar wiwi da kwayar Exol guda 96 gami da kwayar D5 guda 28 gami da Tramol da dai sauransu.

A halinda ake ciki an kammala bincike Kuma an hannanta Wanda ake zargin ga Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Kasa dake Katsina.

Daga bisani Kwamandan Hukumar ta NSCDC a Jihar Katsina ya hori masu aikata laifukan ta’addanci da sauran laifuka a Jihar da su kauracewa hakan tare da horon jama’a da su kasance masu sa ido akan duk wani da suke zargi da aikata laifi a yankunansu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: