Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Sarkin Daura ya nada Shugaban hukumar NIMASA Chiroman Hausa 
Sarkin Daura ya nada Shugaban hukumar NIMASA Chiroman Hausa 

Sarkin Daura ya nada Shugaban hukumar NIMASA Chiroman Hausa 

0

Sarkin Daura ya nada Shugaban hukumar NIMASA, Dr. Bashir Jamoh, Chiroman Hausa 

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya nada Shugaban hukumar dake kula da zirga-zirga da kuma tsaron hanyoyin Ruwan Najeriya watau Nigerian Maritime Administration and Safety Agency (NIMASA), Dr. Bashir Jamoh, a matsayin Chiroman Daura.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke days sa hannun Sarkin da kan sabbin da kuma kwanan wata na 6 ga watan Satumba da jaridar Katsina Post ta gani.

A takardar, Sarkin ya ce sun zartar da hukuncin baby shirts sarautar ne sakamakon so da biyayyar sa ga Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari GCFR da kuma gudummarwar da yake bayarwa wajen cigaban zirga-zirgar Jiragen Ruwa akowane lungu da sako na da’irar ruwa mallakin Najeriya.

Takardar ta kara da cewa nasarar daya samu a fannin tabbatar da kyakkyawan yanayi a wannan fanni a bayyane suke kuma ya bada gagarumar gudummawa wajen samun nasarar aiwatar da kudurorin da Gwamnatin Shugaban Muhammadu Buhari GCFR (Bayajida II) ta sanya a gaba a wannan fanni, duk da komabayan da Annobar Covid 19 ta haifar a duniya baki daya.

Daga karshe, Sarkin ya yi fatan cewa wannan sarautar ta kara masa zumma wajen cigaba da bayar da irin wannan gudummawa dan dorewar bunkasar tattalin arzikin wannan Kasa tamu ta Najeriya.

Sai kuma ya shaida masa cewar anan gaba za’a gudanar da bikin nada maka wannan sarauta bayan an cimma matsaya tare a kan rana da lokacin da za’a gudanar da bikin nadin.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: