Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Gwamna Masari ya ci amana ta, na goge lambobin sa daga waya ta – Inji Tata
Gwamna Masari ya ci amana ta, na goge lambobin sa daga waya ta – Inji Tata

Gwamna Masari ya ci amana ta, na goge lambobin sa daga waya ta – Inji Tata

0

Gwamna Masari ya ci amana ta, na goge lambobin sa daga waya ta – Inji Tata 

Tsohon dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Katsina na jam’iyyar APGA a zaben shekarar 2015, Alhaji Umar Abdullahi wanda aka fi sani da Tata ya ce Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya saba amanar da suka kulla da shi.

Haka ma dan Siyasar ya bayyana cewa tun bayan zaben shekarar 2019 ne ya goge lambobin Gwamnan are wayar sa.

Tata ya bayyana hakan ne a cikin wani dogon rubutun da ya wallafa a turakar sa ta dandalin sadarwar zamani ta Facebook database sanyin safiyar Litinin days kuma jaridar Katsina Post ta gani ta kuma karanta.

A cikin dogon rubutun mai taken ‘AFUWWAN MAI GIRMA GWAMNA WANNAN MAGANAR BA HAKA TAKE BA!’ Tata ya musanta wasu maganganu da yace anyi a ofishin Gwamnan na cewa wai ya aikawa Gwamnan sakon Kar-ta-kwana a wayar sa yana so Gwamnan ya sai masa ragon layya.

Ga dai cikakken rubutun nan da muka tsakuro:

AFUWWAN MAI GIRMA GWAMNA WANNAN MAGANAR BA HAKA TAKE BA!

A yau ake gaya mani cewar ya Mai girma gwamna sakamakon shawarar da na bayar ga gwamnatin ka a kan harkar tsaro, ka nuna ma wasu gungun mutane a cikin office dinka wayar ka cewa wai ni Tata, nayi maka text message in da na nemi ka sai mani ragon layya wanda ka ki ka sai mani, wanda a cewar ka shine yayi sanadiyyar rubutun da nayi na shawarar dana baka a kan security.

Ya mai girma gwamna kai uba ne kuma har gobe ina yi maka kallon haka. Babbar matsala ta da kai da kaki ka gane hakan. Wannan ne dalilin da yasa kasa a ka ci mani mutunci a jaridu na Nigeria saboda kawai na shiga harkar tsaro ta Dutsinma don kare rayuwar al’umma ta. Maimakon in baka son wannan aikin da nike yi wanda sau biyu ina samun ka a office a kanshi da akwai mutuntatwa sai ka kira ni ko ka aiko mani a matsayin ka na shugaba na da nike yi ma biyayya cewa in bari baka so. Wallahi ko daki ka saka ni ka doke ni, in har abinda nike yi laifi ne ka isa tunda babu wanda ya sani. Amman kasancewar kafi karfin ka bani wannan darajar, ka umurci a aikata abinda ya sa6a amanar da muka kulla ni da kai in da muka sa Allah mahilliccin Saraki a matsayin sheda. Cin mutunci baya cikin amana!

Daga wannan ranar ni kuma na yanke hukuncin cewa har abada na gama taka in da kake. Don ni ba a ta6a ci mani mutunci a wuri ba kuma na koma. Yau shekara daya kenan rabon na da taka inda kake! Ta yaya kuma zan nemi rago daga wajen mutumen da na kaurace mawa? Haba mai girma NA RANTSE MAKA DA ALLAH, WALLAHI TALLAHI BILLAHI TUN 2019 NA GOGE WAYOYIN KA A LAYI NA. So Wallahi tallahi billahi in wani yayi maka text na neman rago ba ni bane. Kuma ni ba karamin mutum bane da zan yi hushi a kan rago don wallahi na rasa abinda yafi rago a rayuwa kuma ina zaune lafia. Abinda kayi mani a baya wallahi nagode kwarai amman rago dai ka nemi wanda yayi maka text bani ba.

Maganar kuma cewa bani da kudin takara ya mai girma gwamna ai mulki na Allah ne. Ka nema kana da kudi da iko a matsayin ka na Speaker (No.4 a Nigeria) a 2007 mai badawa bai baka ba. A 2015 baka da ko sisi kuma ya baka gamu masu kudin bai bamu ba. Kila rashin kudi yana daga cikin criteria ta ubangiji na bada mulkin jihar Katsina. In haka ne IT IS. MY TURN inshaa Allahu. Zamu nema gare Shi tunda babu abinda ake biyan shi ya bayar Inshaa Allahu. Wamaan yattaqillaha yajallahu makraja. Wa yarzuqhu min haisu la yahtasib. Wamaan yatawakkalu alallah fahuwa hasbuhu!

Wannan shine dogaro na ya mai girma gwamna. Da fatan Allah yasa ban bata maka rai ba.

Nagode kwarai!

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: