Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An fara shari’a tsakanin Sakataren Gwamnati Dr Mustapha Inuwa da Alh. Musa Muhd Danmusa
An fara shari’a tsakanin Sakataren Gwamnati Dr Mustapha Inuwa da Alh. Musa Muhd Danmusa

An fara shari’a tsakanin Sakataren Gwamnati Dr Mustapha Inuwa da Alh. Musa Muhd Danmusa

0

A yau litinin aka fara sauraren sharia tsakanin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Dr. Mustapha Inuwa da shugaban Gwagware Foundation na Karamar Hukumar Dan-Musa, Alhaji Musa Muhammad.

An saurarin karar ne a Kotin Majistire dake a cikin Katsina.

Binciken Jaridar Katsina Post ya gano cewa Mustapha Inuwa ya shigar da karar ne a bisa zargin Musa Muhammed da kokarin bata mashi suna acikin wani faifan murya da majiyar taji.

A cikin faifan muryan anji wani na jawabi a bisa zargin sakataren Gwamnatin da masaniya game da al’amurran rashin tsaro daya addabi fadin jihar Katsina, lamarin da wanda ake zargi ya musanta.

Alhaji Musa Muhammad dai tuni yasha musanta zargin tare da alkanta tuhumar da tsamar siyasa dake tsakaninshi da Sakataren gwamnatin, kamar yanda majiyarmu ta binciko.

Lauyan wanda ake Tuhumar, Barista Peter Israel yayi ma majiyarmu karin haske bayan da aka kammala sauraren shariar a kotu.

Israel ya shaida ma wakilinmu cewa wanda ake tuhuma yace bashi da hannu wajen yi ko watsa faifan muryar.

Ya kara da cewa yanzu haka yana hada hujjuji da zasu gamsar da kotu cewa wanda ake zargi bashi da laifi.

Kuma a cewarshi ya nemi kotu da ta bashi dama domin samar da hujjojin da zasu wanke wanda ake tuhumar.

Wani makusancin wanda ake tuhuma daya bukaci a sakaya sunanshi ya bayyana ma jaridar Katsina Post irin tsamar dake tsakanin sakataren Gwamnatin da Alhaji Musa Muhammad.

Ya bayyana cewa “Tuni dama akwai tsama a tsakaninsu dalilin bambancin siyasa”.

” Shi Musa hadimine na Dikko Umar Radda wanda kuma abokin hammayyane gashi Mustapha Inuwa”.

“Akwai lokacin baya dashi Mustapha Inuwa ya tabayi ma Musa Muhammad transfer daga Danmusa ya maidashi Bindawa, Lamar in day a’s har Dikko Radda yayi magana da Maigirma Gwamna dangane da lamarin”.

Katsina Post ta gano cewa Alhaji Musa Muhammad kwanakin baya a karkashin gidauniyar Gwagware Foundation ya aiwatarda rabon kayayyakin abinci ga marayu da yan’gudun hijira dake yankin karamar hukumar DanMusa.

Mun tun tibi Kabir Usman Amoga, shugaban Gidauniyar Gwagware a Jihar Katsina ya tabbatar mana da lamarin.

Ya kuma sheda ma wakilinmu cewa Alhaji Musa Muhammad ya share akalla kwanaki goma a tsare wajen jami’an tsaro kamin yau a gabatar dashi a gaban alkali.

Ya bayyana cewa duk da shike zargi ne babu tabbacin wanda ake tuhuma ya aikata, da irin kokarin da sukayi na ziyartar sakataren gwamnati har gida domin sasanta lamarin.

Mun nemi jin ta bakin lauyan mai gabatar da kara Barista Ernest Obunadike abin yaci tura.

Alkali ya dage shariar zuwa ranar 27 ga wata domin cigaba da sauraren sharia.

 

 

 

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: