Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Latest Rochas zai tallafawa makarantun allo 500 da malaman su a Katsina
Rochas zai tallafawa makarantun allo 500 da malaman su a Katsina

Rochas zai tallafawa makarantun allo 500 da malaman su a Katsina

0

Rochas zai tallafawa makarantun allo 500 da malaman su a Katsina 

Akalla Daliban Makarantun Allo su 500 da Malamansu ne zasu amfana da tallafi domin nuna murnar cika shekaru 59 a gidan duniya da Senator Rochas Okorocha zai gudanar nan ba da jimawa ba a Jihar Katsina.

Babban Jami’in Gidauniyar Rochas Care a Jihar Katsina kuma Shugaban rukunin kamfanonin Gafai Communication, Alhaji Musa Gafai ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook cewa za’a gudanar da bada wannan tallafi.

Bayar da tallafin na daya daga cikin dumbin ayyukan jin kan al’umma da Gidauniyar ta Rochas Care ke gudanarwa a fadin kasarnan.

Haka zalika tallafin wata yar manuniya ce dake nuni da tausayawa da Sanatan yake yi ga Almajirai da Malamansu domin su san cewa al’umma ta kula da su.

Idan dai za’a iya tunawa,Gidauniyar ta Rochas Care tana gudanar da ire-iren wadannan ayyuka na jin kan al’umma a lokuta daban-daban a Jihar Katsina da sauran sassan kasarnan.

A Jihar Katsina bisa ga samun Shugaba Jajirtacce Alhaji Musa Gafai,Gidauniyar tana gudanar da ire-iren ayyukan na jin kan al’umma daga lokaci zuwa lokaci.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: