Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Gidauniyar SDA ta yaye dalibai 33 da ta koyama sana’oi a Katsina
Gidauniyar SDA ta yaye dalibai 33 da ta koyama sana’oi a Katsina

Gidauniyar SDA ta yaye dalibai 33 da ta koyama sana’oi a Katsina

0

Gidauniyar SDA ta yaye dalibai 33 da ta koyama sana’oi 

Gidauniyar SDA dake da mazauni a garin Dandagoro na karamar hukumar Batagarawa ta yaye dalibai talatin da uku (33) da suka koyi sana’oin hannu daban daban.

Gidauniyar wadda Alhaji Shamsu Dahiru ke jagoranta ta yi bikin yaye daliban ne a ranar Lahadi a farfajiyar makarantar dake a garin na Dandagoro.

Katsina Post ta samu cewa daliban da suka anfana duka mata ne kuma sana’oin da suka koya sun hada da hada takalma da jikkuna na mata da sarrafa fulawa da kuma dinki.

Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban gidauniyar ya bayyana cewa nan gaba gidauniyar zata fadada ayyukan ta inda za ta dauki dalibai maza domin bada gudummuwar wajen rage rashin aikin yi da kuma zaman banza a tsakanin su.

Shima da yake tofa albarkacin bakin sa, Magajin Garin Dandagoro, Alhaji Muttaqha Magaji ya yabawa Shugaban gidauniyar inda kuma ya yi kira ga masu hannu da shuni su kwaikwayi irin wannan aikin Alheri domin cigaban al’umma.

Suma daliban wadanda suka yi jawabi a wurin taron sun yaba ma Shugaban gidauniyar tare kuma da Shan alwashin za su cigaba da rike sana’ar ta su da muhimmanci domin dogaro da kan su da kuma taimakon sauran al’umma baki daya.

Taron ya samu halartar manyan mutane da suka hada da Magajin Garin Dandagoro Alhaji Muttaka Magaji, Alhaji Ummaru Lemah Batagarawa, Wakilin Kwamishinan ayyuka Hon. Tasi’u Dahiru Dandagoro, Hajiya Jamila Salman, Dr. Garba Isyaku Dan Tutture Ma ga Takarda na kwalejin Ilmi ta Gwamnatin Tarayya dake Katsina, Mai Taimakawa Gwamna Masari Saifullahi Dandagoro, Nura Dahiru Ahmed da dai sauransu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: