Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An kama babban dan ta’addan da aka dade ana nema a Katsina
An kama babban dan ta’addan da aka dade ana nema a Katsina

An kama babban dan ta’addan da aka dade ana nema a Katsina

1

An kama babban dan ta’addan da aka dade ana nema a Katsina 

Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya dake a jihar Katsina sun yi nasarar kama wani gawurtaccen dan ta’adda da aka dade ana nema a Katsina.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar yan sandan a Katsina, SP Gambo Isah ya shaidawa yan jarida, dan ta’addan sunan sa Awwal Aliyu kuma dan asalin karamar hukumar Paiko ne ta jihar Neja dake a Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Dan ta’addan mai shekaru kimanin 32 a duniya wanda kuma aka fi sani da Dan Kalli, an kama shi ne a garin Batsari ta jihar Katsina a farkon watan nan na Satumba.

Da yake karin haske ga manema labarai, SP Gambo Isah yace an samu nasarar cafke Dan Kalli a tashar motar garin Kurfi lokacin da yake kokarin sulalewa ya bar garin na Batsari bayan yin wasu uzourorin sa.

Sai dai ya kara da cewa yan sandan da suka kama shi sun samu layukan waya akalla guda shida da kuma shaidar zama dan kungiyar yan banga na bogi da kuma kayan sawar su.

SP Gambo Isah ya ce yanzu haka suna cigaba da binciken sa da zummar gurfanar da man shi gaban kuliya.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: