Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Miyetti Allah Kautal Hore Ta Nisanta Kanta Daga Kalaman Sakataren Su Na Kasa Kan Masari 
Miyetti Allah Kautal Hore Ta Nisanta Kanta Daga Kalaman Sakataren Su Na Kasa Kan Masari 

Miyetti Allah Kautal Hore Ta Nisanta Kanta Daga Kalaman Sakataren Su Na Kasa Kan Masari 

0

Miyetti Allah Kautal Hore Ta Nisanta Kanta Daga Kalaman Sakataren Su Na Kasa Kan Masari 

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, reshen jihar Katsina ta nisanta kanta da kalaman batanci da sakataren kungiyar na Kasa Sale Alhassan yayi da ya kira Masari da ‘tantirin mashayi.

Sakataren kungiyar reshen jihar Katsina Hassan Kuraye ya shaida cewa ba da yawun su sakataren kungiyar Miyetti Allah ya yi wannan kalamai ba.

“Ko bayan ya yi kalaman mun kira shugabannin uwar kungiyar suma sun shaida mana cewa ba da yawun kungiya ya yi wannan magana ba.”

Kungiyar ta aika da sakon bada hakuri ga gwamna sannan ta ce za ta kawo masa ziyara ta musamman tare da sauran shugabannin kungiyar ta Ƙasa domin a baiwa Masari hakuri.

Sakataren Kungiyar Miyetti Allah ta ƙasa Saleh Alhassan ya maida wa gwamnan Katsina Aminu Masari da martani ba sa cewa da yayi,Fulani ne akalla kashi 70 suke ayyukan hare-hare da kashe-kashe a faɗin kasar nan.

Masari ya faɗi haka ne a hira da yayi da talbijin ɗin Channels.

Sai da faɗin haka bai yi wa sakataren Kungiyar Miyetti Allah daɗi ba, sai ya maida masa da martanin cewa shima gwamnan ‘Ɗan maskewa ne’

Jigar Katsina kamar jihar Zamfara na fama da tsananin hare-haren ƴan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma.

Sai dai kuma a cikin makonnin biyu da suka wuce sojojin Najeriya sun bi su har cikin ƙungurmin daji suna ragargazar su.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: