Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Latest Kuyi Ta Kanku Matasa Masu Sha’awar Siyasa A Wakilin Arewa ‘A’ Kafin Lokaci Ya Kure Maku – Daga Usman Muttaka
Kuyi Ta Kanku Matasa Masu Sha’awar Siyasa A Wakilin Arewa ‘A’ Kafin Lokaci Ya Kure Maku – Daga Usman Muttaka

Kuyi Ta Kanku Matasa Masu Sha’awar Siyasa A Wakilin Arewa ‘A’ Kafin Lokaci Ya Kure Maku – Daga Usman Muttaka

0

Kuyi Ta Kanku Matasa Masu Sha’awar Siyasa A Wakilin Arewa ‘A’ Kafin Lokaci Ya Kure Maku – Daga Usman Muttaka

Founder: Katsina Youth Awareness and Mobilisation Forum (KYAMF)

Usman Muttaka

Jagoran Chanji

Umuttakamagaji@yahoo.com

Gaisuwa tare da fatan alkhairi ga al’ummar Jihar Katsina baki daya, muna addu’ar Allah ya kawo mamu zaman lafiya mai dorewa a Jihar mu ta Katsina dama sauran Jihohin Nigeria dake fama da matsalar rashin tsaro. Ni Usman Muttaka da akafi sani da Jagoran Chanji Shugaban Kungiyar (Katsina Youth Awareness and Mobilisation Forum) ina so inyi amfani da wannan kafa domin tunatar da yan uwana abokan gwagwarmaya fagen Siyasa, wanda mafi akasari ‘yayan talakkawa ne iri na, da suyi karatun ta natsu kan salan siyasar wasu mutane, masu da’awar cewa su Elders ne a jam’iyyar mu mai albarka ta APC, a mazabar mu ta (WAKILIN AREWA ‘A’) dake cikin karamar hukumar Katsina.

Salon Siyasar wannan mazaba ta (WAKILIN AREWA ‘A’) abun takaici ne, da rashin tausai, kana akwai tada hankali matuka kan yarda ake tafiyar da hidimar Siyasar a wannan Maza ba , kusan tunda mukai wayau kan lamarin Siyasa, masu rike da ragamar Siyasa wannan Yanki ,mafi yawan su basu damu da inganta rayuwar Matasa ba, takansu kawai suke sai kuma abunda suka haifa.

Saboda da rashin adalci irin nasu, basu damu da samar ma Matasa aiki ba, duk da cewa akwai masu shedar kammala karatu wanda ya hada da DIPLOMA, NCE, DEGREE harma da MASTERS, kana basa iya tallafa ma wanda basu da karfi domin tafiyar da karatun su, amma da zaran anfara Siyasa, lokacin za’a nuna ma Matasan su na da kima da daraja, ana gama Siyasa shikenan sai kuma wata Siyasar ta kunno, wannan rashin Adalci ne kuma ba dai dai bane, kuma dole a gyara ko kuma mu fito mu gayama Gwamnati halin da (Wakilin Arewa ‘A’) take ciki.

Mun tanadi duk wasu hujjojin da ya kamata mu tanada, kan irin rashin san cigaba da wasu Elders suke nuna ma Matasan (WAKILIN AREWA ‘A’), sauran mazabu ba haka abun yake ba, dan kuwa suna neman cigaban Matasan su. Mu Yan APC ne kuma ko da mukami, ko bamu muna nan daram dam, babu gudu babu ja da baya.

Muna kira ga Maigirma Gwamna Rt. Aminu Bello Masari, da ya sani mafi yawan masu rike da Ragamar Siyasar a mazabar (WAKILIN AREWA ‘A’) dake bugun gaba suna cewa sune Elders na APC, wasun su basa amfanar Matasa ko kadan kuma basa neman Cigaban Matasan, ta hanyar bullo da wasu hanyoyi wanda zasu inganta rayuwar Matasan, bayan muna gani a sauran mazabu yarda manyan su ke kokarin samar ma Matasa aikin yi, dama taimakun su kan harkokin karatun su, dan ganin sun zama mutane nagari da Al’umma zasu yi alfahari da su, dan kauce ma fadawa Shaye – Shaye, tare da aikata manyan laifuka.

Allah yasa mugane dai – dai ya kuma doramu kan dai dai, ya gafarta mamu dukkanin kurakuran mu baki daya, ya zaunar da Jihar lafiya dama kasar baki daya Amin.

Mungode

Daga Shugaban Kungiyar (KYAMF)

MUTASHI MU NEMI YANCIN KAN MU DA KAN MU MATASAN MAZABAR (WAKILIN AREWA ‘A’)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: