Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Majalisar zartarwar jihar Katsina ta amince ta sabon kalar fentin motoci da kurkurori
Majalisar zartarwar jihar Katsina ta amince ta sabon kalar fentin motoci da kurkurori

Majalisar zartarwar jihar Katsina ta amince ta sabon kalar fentin motoci da kurkurori

1

Majalisar zartarwar jihar Katsina ta amince ta sabon kalar fentin motoci da kurkurori

Gwamnatin Jihar Katsina tana kara godiya da jinjina ga al’umma bisa ga fahimta, goyon baya da kuma gudummawar da suke badawa wajen yaki da ta’addanci da kuma ‘yan ta’adda.

A dayan bangaren kuma Majalisar ta zartaswa ta amince da irin kalolin fentin da za ayi wa motoci da kurkurori na haya da ake amfani dasu a fadin jihar nan.

Kalolin dai sune kalar dorowa wadda bata ciza ba (light yellow) da kuma kalar bula ita ma wadda bata ciza ba (light blue).

Haka kuma za a fitar da alamomi da kuma lambobin da za su banbance su tsakanin kananan hukumomin da suka fito. Kwamishinan Ayyuka da gidaje ya bayyana hakan a yayin wannan zama da akayi da manema labaru, tare da cewa hakan duk yana cikin kokarin tsare lafiya da dukiyoyin al’ummar jihar nan.

Wannan na kunshe cikin bayanin bayan taron Majalisar zartaswa ta jiha da akayi yau a babban dakin taro na Gidan Janar Muhammadu Buhari, fadar Gwamnatin Jihar.

Majalisar kuma ta ce, ganin yadda al’umma suke nuna fahimta ga matakan da Gwamnati ke dauka na dakile ta’addanci tare kuma da yin hobbasa wajen kare kai, ya zama wajibi ayi masu godiya ta musamman domin a zaburar dasu, domin duk nasarar da aka samu da goyon bayan su aka same ta.

Haka kuma, gwamnati, tana jan hankalin al’umma da suka sa ido sosai wajen gano bata garin cikin mu da suke aike ma ‘yan ta’adda da bayanai (informers) domin hadarin su yafi na masu ta’addancin domin su ke bada bayanan da masu ta’addancin suke amfani dasu suna ma al’umma zilla.

 

Mai ba Gwamna Shawara a kan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina wanda ya yayi wani jawabi, ya bada tabbacin cewa aikin da aka fara da kananan hukumomin Jibia da Batsari, za aci gaba dashi har sai an tabbatar da an kakkabe ‘yan ta’addar da suka addabi al’umma.

 

A daya bangaren kuwa, Majalisar zartaswar ta amince da irin kalolin fentin da za ayi wa motoci da kurkurori na haya da ake amfani dasu a fadin jihar nan. Haka kuma za a fitar da alamomi da kuma lambobin da za su banbance su tsakanin kananan hukumomin da suka fito. Kwamishinan Ayyuka da gidaje ya bayyana hakan a yayin wannan zama da akayi da manema labaru, tare da cewa hakan duk yana cikin kokarin tsare lafiya da dukiyoyin al’ummar jihar nan.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: