Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Gwamnatin Katsina ta rufe haramtattun tashoshin mota na kan hanya
Gwamnatin Katsina ta rufe haramtattun tashoshin mota na kan hanya

Gwamnatin Katsina ta rufe haramtattun tashoshin mota na kan hanya

0

Gwamnatin Katsina ta rufe haramtattun tashoshin mota na kan hanya 

Masari ya rufe haramtattun tashoshin mota na kan hanya a Katsina 

Majalisar zartaswar jihar Katsina ta amince da rufe haramtattun tashoshin mota na kan hanya a cikin fadin jihar Katsina.

Wannan matakin na majalisar an dauke shi ne a yayin zaman ‘yan majalisar karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ranar Larabar da ta gabata.

Majalisar ta ce wannan matakin an dauke shi ne da nufin kara tabbatar da dokar nan da Gwamnan jihar ya sanya ma hannu a satin da ya gabata.

Haka zalika majalisar, a cikin wata sanarwar yada labarai daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar, ta umurci dukkan motocin haya da motocin safa-safa da su gaggauta komawa cikin halastattun tashoshin motocin dake a jihar.

Haka ma kuma majalisar zartarwar ta ce dole ne daga yanzu masu tuka baburan haya su rika sanya riguna masu kyalkyali domin tantancewa.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: