Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Mafi yawancin ‘yan bindiga Fulani ne dake ikirarin bin addinin Musulunci kamar ni – Masari
Mafi yawancin ‘yan bindiga Fulani ne dake ikirarin bin addinin Musulunci kamar ni – Masari

Mafi yawancin ‘yan bindiga Fulani ne dake ikirarin bin addinin Musulunci kamar ni – Masari

0

Mafi yawancin ‘yan bindiga Fulani ne dake bin addinin Musulunci kamar ni – Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce yawancin ‘yan bindiga sun fito daga kabilar Fulani ne kamar shi, inda ya kara da cewa suna yin yaren Fulfulde, kuma suna bin addinin Musulunci kamar yadda shi ma yake bi.

Ya ce ya san cewa da yawa daga cikin ‘yan Arewa ba za su ji dadin wannan magana ta shi ba, amma dai ya san abinda ya fada gaskiya ne.

Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Litinin, a lokacin da ya kai ziyara gidan Talabijin na Channels, inda yayi hira a cikin shirin ‘Politics Today’, ma’ana ‘Siyasa a Yau’, wanda jaridar Punch ta nada.

Da aka tambaye shi dangane da ko su waye ‘yan bindigar da suka hana kowa sakat a yankin Arewa maso Yamma dama kasa baki daya, Masari ya ce:

“Mutane ne iri na, da suke yare irin nawa, kuma suke bin irin addinin dana ke bi.

“Saboda haka abinda muke da su a yanzu, ‘yan bindiga ne; ba dodanni bane, mutane ne da muka sani, mutane ne dake zaune da mu shekaru aru-aru.

“Haka kuma wadanda suke haurowa daga wasu kasashe na nahiyar Afrika ta Yamma, da Afrika ta Arewa, suma kabilar Fulani ne.

“Da yawa daga ciikin wadanda ke da hannu a ta’addanci Fulani ne, koda hakan ya yiwa wasu dadi ko bai yi ba, wannan ita ce gaskiya. Ba wai na ce dukkan su Fulani bane, amma tabbas yawancin su Fulani ne, kuma sune mutanen dake zaune a daji, aikin su kuma shine kiwon shanu.”

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: