Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Masari na son a datse layukan sadarwar kananan hukumomi 13 a Katsina
Masari na son a datse layukan sadarwar kananan hukumomi 13 a Katsina

Masari na son a datse layukan sadarwar kananan hukumomi 13 a Katsina

0

Masari na son a datse layukan sadarwar kananan hukumomi 13 a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya ce gwamnatin sa ta rubutawa hukumar sadarwar Najeriya watau Nigerian Telecommunications Commission a turance takarar bukatar datse layukan sadarwa a kananan hukumomi akalla 13 na jihar ta Katsina.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata fira da yayi da gidan talabijin din Channels wadda suka watsa a ranar Litinin da daddare wadda kuma Katsina Post ta bibiya.

A cikin firar, Gwamna Masari yace manyan makiyan al’umma musamman a kokarin da gwamnati ke yi wajen ganin n samu zaman lafiya sune masu ba ‘yan bindiga bayanai na sirri.

Yace su kuma su masu bada bayanan sirrin suna zaune ne a cikin al’umma a wasu lokutta ma har a cikin jami’an tsaron mu.

Sai dai Gwamnan da aka tambaye shi ko zai so a rufe layukan sadarwa a jihar ta Katsina kamar yadda aka yi a jihar Zamfara, sai ya ce a’a shi ba ya goyon bayan a datse layukan sadarwar a dukkan jihar.

“A a ban goyon bayan a rufe layukan sadarwar duka jihar amma tuni ma har mun rubutawa hukumar sadarwa ta kasa cewar a rufe layukan sadarwar a kananan hukumomin da ke makwaftaka da daji domin tabbatar da nasarar aikin da aka fara”, Inji Gwamnan.

Sai dai Gwamnan bai lissafa kananan hukumomin guda 13 din ba a cikin firar.

Amma Jaridar Katsina Post ta san cewa kananan hukumomi kamar Jibia, Batsari, Danmusa, Kankara, Faskari, Sabuwa da Dandume duka sun yi iyaka da dazuzzukan da ke zama maboya ga ‘yan bindiga.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: