Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace kanwar mataimakin kakakin majalisar Katsina
Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace kanwar mataimakin kakakin majalisar Katsina

Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace kanwar mataimakin kakakin majalisar Katsina

0

Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace kanwar mataimakin kakakin majalisa a Katsina

Wasu’ yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun shiga garin Tafoki dake karamar hukumar Faskari kuma suka sace kanwar kakakin majalisar jihar Katsina, Alhaji Shehu Dalhatu Tafoki.

Kamar dai yadda majiyar mu ta dailytrust.com ta ruwaito, kanwar ta mataimakin kakakin majalisar mai suna Asma’u Dalhatu an sa mata biki kuma har an fara shire-shiren aurar da ita kafin lamarin ya faru a jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Honorable Dalhatu Tafoki ya bayyana cewa a daren ranar Lahadin ne ‘yan bindigar suka shiga garin na Tafoki kuma suka kutsa kai gidan mai Unguwar garin wanda nan ne gidan su kuma suka dauke’ yan mata biyu suka shiga daji da su.

Sai dai ya bayyana cewa a kan hanyar su, yan bindigar suka hadu da wasu yan sintiri wadanda suka tafka gumurzun har daya daga cikin matan ta tsere.

Honorable Tafoki ya kara da cewa ya zuwa yanzu dai ba a tuntube su ba domin neman kudin fansa.

 

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: