Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Gwamnatin jihar Katsina ta hana sana’ar cajin waya a kananan hukumomi 19
Gwamnatin jihar Katsina ta hana sana’ar cajin waya a kananan hukumomi 19

Gwamnatin jihar Katsina ta hana sana’ar cajin waya a kananan hukumomi 19

3

Gwamnatin jihar Katsina ta hana sana’ar cajin waya a kananan hukumomi 19

Gwamna Masari ya hana sana’ar cajin waya a kananan hukumomi 19

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kafa dokar hana sana’ar cajin wayoyi a kananan hukumomi goma sha tara (19).

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a gidan gwamnatin jihar yayin kaddamar da kwamitin da zai sa ido akan dokar nan ta lalubo zaman lafiya da ya sa ma hannu a satin da ya gabata.

Kamar yadda Gwamnan ya zayyana, kanakan hukumomin da wannan sabuwar dokar ta shafa sun hada da Kaita, Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Faskari da Sabuwa.

Sauran kananan hukumomin sun hada da Funtua, Dandume, Bakori, Danja, Malumfashi, Kafur, Musawa da Matazu.

Haka zalika dokar, kamar yadda Gwamnan ya bayyana zata hada da kananan hukumomin Dutsin-ma, Kurfi da kuma Mai’adua.

A cikin jawabin na Gwamnan, ya kuma bayyana cewa, a Karon farko, gwamnatocin jihohin dake makwabtaka da dajin rugu, sun daki alkibla daya wajen tunkarar ta’addancin da ya addabi jihohin na Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna da Naija.

Gwamnan ya kara da cewa, a yanzu, babu wani abu da gwamnati ta tasa a gaba irin dawo da zaman lafiya tabbatacce a fadin wannan jiha.

Ya kuma yi kira ga ‘yan wannan kwamiti da suyi amfani da matakin ba sani ba sabo wajen gudanar da wannan aiki, kuma suyi kokarin wayar da kan al’umma kan muhimmancin dake akwai wajen dabbaka wadannan dokoki, domin an kafa su ne domin ceto rayuka da dukiyoyin su.

Ya kuma yi kira ga al’umma dasu daure suci gaba da tona asirin masu kai ma ‘yan ta’adda bayanai (informers) da kuma masu kai masu kayan amfanin yau da kullum.

Ta bangaren shi, Shugaban kwamitin Alhaji Sanusi Buba, wanda kuma shi ne Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Katsina, ya tabbatar wa Gwamna Masari cewa za suyi duk abinda ya kamata domin ganin an cimma burin kafa wannan dokoki, wanda shi ne dawo da zaman lafiya a cikin wannan jiha.

A satin da ya gabata ne, Gwamna Aminu Bello Masari ya sanya hannu a kan wasu sabbin dokoki da za su taimaka wajen yaki da ta’addanci. Dokokin sun hada da na rufe wasu kasuwanni, takaita zirga zirgar ababen hawa, takaita yawan gidajen da za su saida mai a kananan hukumomin da matsalar tafi kamari.

Wakilan kwamitin sun hada da Mai ba Gwamna Shawara a kan sha’anin Tsaro, Wakilan Masarautar Katsina da ta Daura, wakilin rundunar Sojoji, wakilin Hukumar Samar da tsaro ta farin kaya (NSCDC), wakilin hukumar hana sha da fataucin kwayoyi (NDLEA).

Haka kuma a matakin kananan hukumomi, akwai irin wannan kwamiti a karkashin Baturen ‘Yan Sanda (DPO) na karamar hukumar.

Comment(3)

  1. To Allah yabada Hakuri ga wadanda wannan dokokin suka shafa,kuma Allah yakawo mana zaman lapiya mai dorewa akasarmu Baku daya

  2. Masha Allahu yanzu muntabbatar dagaske akeyi wurin kokarin dakile wanna matsalar Allah yataimaka yabada nasara

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: