Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Yan Charanchi sun koka kan dokar hana sayar da babura a kasuwar garin
Yan Charanchi sun koka kan dokar hana sayar da babura a kasuwar garin

Yan Charanchi sun koka kan dokar hana sayar da babura a kasuwar garin

1

Yan Charanchi sun koka kan dokar hana sayar da babura a kasuwar garin 

Wani mazaunin Charanchi ya bayyana takaicinsa na yadda Gwamnatin jihar Katsina ta haramta sayar da sakan han din mashina a kasuwar Charanchi dake nan cikin jihar Katsina.

Kamar yadda ya turo wa Katsina Daily Post News, kokensu suna kira zuwa ga gwamnatin jihar Katsina, da ta dubi lamarin bisa ga yadda a Charanchi ne kadai aka haramta saye da sayar da sakon din babura a duk fadin jihar.

“Yanzun an ce a Charanchi ne kadai aka hana sayar da mashina, kuma an kyale a ci gaba da sayar da su a sauran kasuwannin jihar Katsina, mu yan karamar hukumar Charanchi muna kallon hakan kamar an tauye mana hakki ne, saboda an kyale wasu kasuwannin, amma mu an hana mu.

“Ba muna nuna rashin gamsuwa bane da matakan da gwamna ya dauka don samar da zaman lafiya bane, muna dai son dokar hana sayar da babura a Charanchi da a duba ta, saboda a Charanchi kadai aka sa ta.

“Yanzun duk sauran kasuwannin jihar Katsina irinsu Kafur, da Jibiya Dutsinma Malumfashi da sauran manyan kasuwannin jihar Katsina babu inda aka sa wannan dokar sai a Charanchi, a don haka mai girma Gwamna muma muna kira da a duba mana.

Za a iya tuna cewa dai a ranar 31 ga watan August 2021, Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da wasu sabbin dokoki har guda 12 ciki har da haramta sana’ar bumburutu, da sayar da sabbi, da hana bin wasu hanyoyi, duk domin shawo kan matsalar tsaron da ya addabi jihar ta Katsina.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: