Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Yan bindiga sun fara daukar matasa aiki a kauyukan Katsina
Yan bindiga sun fara daukar matasa aiki a kauyukan Katsina

Yan bindiga sun fara daukar matasa aiki a kauyukan Katsina

0

Yan bindiga sun fara daukar matasa aiki a kauyukan Katsina Inji Gwamna Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari yace yanzu kam ‘yan bindiga suna nema su wuce makadi da rawa inda a wasun su tuni suka fara daukar matasa aiki suna sa su cikin harkar ta’addanci musamman a kauyukan da ke kusa da daji.

Gwamnan ya bayyana hakan ne da yake jawabi ga wata tawagar Sufeto Janar na yan sanda ta musamman da ta kai masa ziyarar aiki ta wuni daya a gidan gwamnatin jihar.

Gwamna Masari ya kuma yi kira ga hukumar ‘yan sandan da sauran jami’an tsaro dasu dauki tsauraran matakai na gaggawa domin kawarda jagororin ‘yan ta’adda, musamman masu fitowa suna gadara da kalaman izgilanci a kafafen sadarwa na zamani.

A cewar sa, yin hakan zai dawo da martabar hukumomin da jami’an tsaron a idon al’umma sannan kuma zai sa’ yan ta’addan su shiga taitayin su domin yanzu suna ganin sun fi karfin kowa.

Haka kuma Gwamnan ya bayyana cewa babu dalilin wani cece kuce a kan kiran da yayi na al’umma su kare kan su, domin kuwa shi yayi magana ne bisa ga fahimtar shi da al’amarin a matsayin shi na Gwamnan Jihar Katsina, su ma wadanda suke nuna rashin aminta da kiran nashi, suna yi ne a kan iya fahimtar su ta masu hangen al’amarin daga nesa.

Ya Jaddada cewa ba fa zai yiwuwa ba mutane suyi zaune ayi ta ci masu zarafi ana kisa ba tare da sun daga hannun kare kai ba, tare da bayyana cewa duk halitta dama can a dabi’a ita ke fara kare kanta daga hari kafin a kawo mata dauki.

Tun farko a jawabin shi, Sufeto Janar Usman Alkali Baba ya shaida wa Gwamna Aminu Masari cewa yazo Jihar Katsina domin ya gani kuma yaji halin da ake a kan yaki da ta’addanci da ake tayi wanda yaki ci yaki cinyewa.

Ya kuma bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin basu duk goyon bayan da suke bukata domin cin nasarar wannan yaki dama sauran ayyukan da rundunar ta ‘yan sandan Najeriya take yi.

Ya ce akwai sabbin tsare tsare da shirye shirye da suka fara shigo dasu domin canza salon yaki da ta’addanci wanda za su kai ga cin nasara.

Alhaji Usman Alkali ya kuma yi ga al’umma da kowa ya tashi tsaye ya bada gudummawar domin aikin samarwa tare da tabbatar da tsaro na kowa ne ba tare da nuna wani banbanci ba.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: