Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Kasuwar Santara: Gwamnatin Katsina ta biya ‘yan kasuwar da suka yi asara
Kasuwar Santara: Gwamnatin Katsina ta biya ‘yan kasuwar da suka yi asara

Kasuwar Santara: Gwamnatin Katsina ta biya ‘yan kasuwar da suka yi asara

1

Kasuwar Santara: Gwamnatin Katsina ta biya ‘yan kasuwar da suka yi asara 

– Ta rabawa’ yan kasuwa 685 Naira miliyan 247

Gwamnatin jahar Katsina ta raba Naira miliyan dari biyu da miliyan arba’in da bakwai 247 a matsayin tallafin ga yan kasuwar Santara (Central Market) su 685 wadanda suka rasa dukiyar su sakamakon gobarar data auku a baya.

Da yake kaddamar da bayar da tallafin, shugaban kwamitin wanda kuma shine Kwamishinan Shari’a Barista Usman EL-MARZUK ya bayyana cewa kudin sun hada da gudumuwar ma’aikatan Gwamnatin jaha dana kananan hukumomi da kuma ta dai-daikun mutane da kungiyoyin da suka bayar domin tallafawa wadanda gobarar ta shafa.

Kamar yadda yace gwamnatin jaha ta yanke shawarar baiwa kowannensu kashi arba’in 40 na abinda sukayi asara domin rage masu radadin da gobarar ta haddasa masu inda ahalin yanzu zasu karbi kashi 68 cikin abinda za’a basu.

Ya kara da cewa ‘yan kasuwar zasu karbi sauran kashi 32 a zagaye na biyu dazarar gwamnatin ta ida karbo sauran gumuwar da akayi mata alkawari daga sauran jama’a da kuma kungiyoyi.

Barista Ahamad EL-MARZUK ya kara da cewa gwamnatin jaha ta kafa kwamitin ne domin gano cikakkun bayanan adadin wadanda gobarar ta shafa domin raba tallafin bisa gaskiya.

Kamar yadda yace gwamnatin jaha ta yanke shawarar bayar da kashi 40 na abinda sukayi asara domin rage masu radadin da suke ciki sakama kon gobarar.

A jawabin nasa, EL-MARZUK ya kuma ce kwmitin ya gudanar da aikinshi bisa gaskiya domin tabbatar da yin adalci ga duk kan wadanda lamarin ya shafa.

Tun farko a jawabin maraba, shugaban karamin kwamitin kuma Mai ba Gwamna Shawara akan cigaban alumma, Alhaji Lawal Aliyu ya bayyana lamarin a matsayin wata kaddara daga Allah tare da jaddada damuwar Gwamna da gwamnatin jaha akan lamarin.

Alhaji Lawal Aliyu ya kuma yabawa hangen nesan gwamnatin jaha bisa tallafawa wadanda gobarar ta shafa.

Ya kara da cewa da zaran gwamnati ta ida karbar sauran gudumuwowin zata ida rabawa wadanda lamarin ya shafa a zagaye na 2.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: