Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Da Duminsa: Masari Ya Kafa Sabbin Dokoki 10 Don Dakile Matsalolin Tsaro A Katsina
Da Duminsa: Masari Ya Kafa Sabbin Dokoki 10 Don Dakile Matsalolin Tsaro A Katsina

Da Duminsa: Masari Ya Kafa Sabbin Dokoki 10 Don Dakile Matsalolin Tsaro A Katsina

3

Da Duminsa: Masari Ya Kafa Sabbin Dokoki 10 Don Dakile Matsalolin Tsaro A Katsina

– Ya rufe hanyoyi 2 da gidajen mai, 

– Ya hana saida dabbobi da saffin babura a kasuwanni, 

– Ya hana hawan babura da ‘yar kurkura da daddare 

Gwamnatin Jihar Katsina a Karkashin Jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta bijiro da sababbin dabaru na dakile matsalar tsaro a Jihar.

Sababbin dabarun na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Gwamnan kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Kasarnan ya bashi karfin daukar irin matakan.

Sababbin dokokin sun hada da:
1. Rufe zirga-zirga akan hanyar Jibia-Gurbin Baure har sai an fitar da sanarwar bude hanyar.

2. Rufe zirga-zirga akan hanyar Kankara-Sheme har sai an fitar da sanarwar budewa.

3. An haramta aikace-aikacen manyan motoci dake dauko icce daga dazuka.

4. An haramta sayar da dabbobi a kasuwannin Batsari, Safana, Danmusa, Jibia, Malumfashi da Dutsinma da Sabuwa da Faskari da Kaita da Kankara da Baure da da Mai’adua da Charanchi gami da Kasuwar Kafur.

5. An haramta fitar motar daukar dabbobi daga Jihar Katsina zuwa wata Jiha a fadin Kasarnan.

6. An haramta daukar mutum Uku akan babur ko mutum fiye da Uku a cikin Kurkura.

7. An haramta sayar da babur na hannu ko tsoho a Kasuwar Charanchi.

8. An maido da dokar takaita amfani da ababen hawa daga misalin karfe 10:00pm na dare zuwa karfe 6:00am na safe a cikin Birnin Katsina sai Kuma karfe 6:00pm na Yamma zuwa 6:00 na safe a Kananan Hukumomi da matsalar tsaro ta shafa.

9. An haramta sayar da man fetur a cikin jarkoki a Gidajen Mai.

10. Gidajen Mai 2 ne kadai aka amincewa su sayar da man fetur da ya wuce na naira dubu 5000 a Kananan Hukumomin Jibia da Batsari da Danmusa da Safana da Kankara da Faskari da Sabuwa da Dandume da Musawa da Matazu da Dutsinma da Kurfi da Danja gami da Karamar Hukumar Kafur.

11. Kamar yadda dokar ta bayyana Ma’aikata na musamman da suka hada da:Ma’aikatan Lafiya da Jami’an Tsaro da Yan Jarida ne kadai aka amince suyi amfani da Kurkura ko Mashin a lokacinda aka shiga lokacin dokar takaita amfani da ababen hawa.

Haka zalika kamar yadda takardar ta bayyana wannan dokoki zasu fara aiki take.

Comment(3)

  1. A gaskiya wannan dokar tayi tsanani dayawa domin hana siye da siyerwa a jahar katsina ba karamar cutarwa bane gamu talakawa, saboda haka ya kamata a duba lamarin a sassauta mana ta bangaren dakatarda 6angaren kasuwanci

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: