Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Al’ummar garin Jibia sun yanke shawarar kai hukumar kwastam kotu
Al’ummar garin Jibia sun yanke shawarar kai hukumar kwastam kotu

Al’ummar garin Jibia sun yanke shawarar kai hukumar kwastam kotu

1

Al’ummar garin Jibia sun yanke shawarar kai hukumar kwastam kotu

Daga: Abdulrazak Ahmad Jibiya

Biyo bayan sanadiyyar mutuwar mutane akalla 10 da raunata akalla 20 da jami’an kwastom suka yi, a ranar 9 ga ogusta 2021, a garin jibia na kara karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

An samu korafafe-korafe da dama daga bangarorin Al’ummar garin da makota, wadanda suka hada da: shugabanni na siyasa da sarauta, ‘yan kasuwa, da sauransu.

Kamar yadda wakilinmu Abdulrazak Ahmad Jibia ya ruwaito, ranar juma’a 27 ga ogustan shekarar, gamayyar kungiyoyin fararen hula reshen karamar hukumar, a karkashin jagorancin kungiyar “Masoya Ci Gaban Karamar Hukumar Jibia” sun gudanar da taron manema labarai inda suka bayyana matsalolin da karamar hukumar ke fuskanta.

Shugaban kungiyar Malam sulaiman kalalu, da ma’aji Alhaji Bishir Adamu, sun nuna damuwarsu game da mummunan halin da ‘yan kasuwa suke ciki na karamar hukumar.

Mamba a kungiyar “JIBIA FIRST” Yusuf Abdullahi (Chana’a), ya musanta jawabin da hukumar kwastom tayi, inda ta karyata labaran dake yawo a kafafen sadarwar zamani cewa “Hukumar ta hana shigar da kayayyakin da aka samar a Najeriya daga birnin katsina zuwa Jibia”. Ya kuma kara da cewa akan idonsa lamarin ya faru.

Wani mazaunin garin jibia Isah Yahuza Dabo, ya nuna damuwarsa game da yadda jami’an tsaro suke amfani da kananan yara (Fararen Hula) wajen gudanar da ayyukansu, kuma ya bayyana makomarsu “a lokacin da suka rasa aikin” a matsayin annoba a cikin al’umma.

Coordinator na kungiyar NYCN reshen karamar hukumar Jibia, Jamilu Hamisu Shalla, ya bukaci gwamnatin najeriya da ta kawar da dokar takaita bude gidajen man fetur da ta saka a kananan hukumomin da suke a iyakokin kasar. Ya kara da cewa “Yin haka zai taimaka wajen magance matsalar tattalin arziki dake addabar kasar.”

Da yake jawabi Ambasadan zaman lafiya na gidauniyar “GLOBAL PEACE FOUNDATION” Comrd. Gidado Sulaiman Farfaru, ya yi kira ga gwamnatin najeriya da tayi gaggawar magance matsalolin da karamar hukumar Jibia ke fuskanta; kuma ya tabbatar cewa matukar hukumar kwastom bata takaita cin zarafin da suke yiwa alummar jibia ba, a shirye suke da su hada kai da manya-manyan kungiyoyin fararen hula na Najeriya domin shigar da kararsu a kotu.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: