Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Gwamna Masari ya canza shawara game da yin gadar sama
Gwamna Masari ya canza shawara game da yin gadar sama

Gwamna Masari ya canza shawara game da yin gadar sama

0

Gadar Sama: Gwamna Masari ya canza shawara 

Gwamna Masari ya canza shawara game da yin gadar sama 

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta canza shawara game da aikin da ta kuduri yi na gina gadar sama watau ‘Flyover Bridge’ a turance har guda biyu a cikin kokuwar birnin Katsina.

Mai karatu da zai iya tuna cewa a cikin watan Nuwambar da ya gabata ne gwamnatin ta ayyana kudurin ta na gina gadar saman a shatale-talen Kofar Kwaya da Kofar Kaura a cikin birnin na Katsina.

Sai dai a yayin taron wayar ma al’umma kai akan kasafin kudin da ake shiryawa na 2022 da ya gudana a dakin taro na tsohon gidan Gwamnati ranar Alhamis din ta gabata, Kwamishinan kasafin kudi da tsare tsare, Hwanarabul Farouk Jobe ya ce yanzu gwamnatin jihar gadar kasa ce za su yi watau ‘Underpass Bridge’ kenan a turance.

Kwamishinan ya kara da cewa yanzu haka gwamnatin ta kammala shirye-shiryen ta domin karbo bashin Naira biliyan 50 daga gwamnatin tarayya wada a ciki ne za a yi wadannan ayyukan tare kuma da kammala wasu ayyukan da ake yi a jihar.

A cewar Kwamishinan, tuni har gwamnatin ta tarayya ta amince da kudurin na gwamnatin jihar.

Hwanarabul Jobe ya kara da cewa ayyukan da gwamnatin ta kuduri aniyar idawa da kudin sun hada da gyaran madatsar ruwan Ajiwa, da ayyukan jawo ruwan dam din Zobe.

Sauran, kamar yadda yace sun hada da gyaran wasu hanyoyi na jihar da kuma kammala gyaran asibitocin da gwamnatin ke yi.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: