Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Buhari yaci amanar mutanen jihar Katsina- Inji Dan Majalisa
Buhari yaci amanar mutanen jihar Katsina- Inji Dan Majalisa

Buhari yaci amanar mutanen jihar Katsina- Inji Dan Majalisa

2

Hon. Aminu A. Garba, Dan Majalisa Mai wailtar Karamar Hukumar Dan-Musa a majalisar dokoki ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yaci amanar mutanan jihar Katsina duba yanda ya gaza kawo karshen matsalar tsaro data addabi jihar.

Karamar hukumar Dan-Musa na daya daga cikin kananan hukumomi da suka fi fama da matsanancin hare-haren yan’bindiga, kasha-kashe, garkuwa da mutane da satar shanu a fadin jihar.

Acikin wani bidiyo da majiyar mu ta Katsina Post ta gani Hon. Aminu A. Garba  acikin kakkausan lafazi yace Shugaba Buhari yaci amanar mutanen jihar Katsina duba da irin tarin kuri’un da suka zuba masa datafi kowace jiha a lokacin zabe.

A WANI LABARIN KUMA: Dan majalissa ya nemi a binciki yanda ake kashe kudaden tsaro a jihar Katsina

Dan. Majalisar ya koka da cewa ko ajiya kafin yayi magana an kashe wani magidanci tare da garkuwa da iyalansa a wani kauyen karamar hukumar da yake wakilta.

Hon. Aminu ya kara da cewa duk da yawaitar jami’an tsaro a Dan-musa bai basu damar murkushe hare-haren yan’ta’adda ba da suka addabi inda yake wakilta.

A cikin jawabin sa Dan-malisar yace “Ni Magana ta kai-tsaye da shugaban kasa zanyi ta. Anci amanar mutanen jihar Katsina sabida mu muka bada kuri’a wadda tafi kowace yawa a Nigeria har ya zama Shugaban kasa.”

“Kamar yanda yan’uwana ke fadi ko a jiya da dare yan bindaga sun shiga cikin garin Dan-Musa wani kauye da ake cema Marken Dambi suka kashe magidanci tare da dauke iyalinshi”.

Ya kara da cewa “Jiya naje Dan-Musa duk wani mai ruwa da tsaki saida mukayi meeting dashi domin kokarin samo hanyar da za’a samu ingattacen zaman lafiya”.

Ya cigaba da cewa “A cikin garin Dan-Musa akwai Jami’an tsaro kusan guda tamanin (80) special squad amman wannan bai hana satar dabbobi ba, garkuwa da mutane ko kasha al’umma. Jiya na fada musu gani gasu da su kwashe kayansu subar garin Dan-Musa”

Dan-Majalisar ya nanata cewa “Ni abunda nake fadi bana regretting saboda al’ummar mu suka zabemu har mukazo majalissa.”

“Ni banda wani gari ko wata dunia daya wuce Dan-Musa amman yanzu ban iya zuwa Dan-musa akan wane dalili?”

“Ana kashe mana mutane, ana kwace musu dukiyoyinsu haka zamu tsaya a matsayinmu na shuwagabanni kullum sai Magana guda muke akan wane dalili?.

Dan Majalisar ya kuma zargin jami’an tsaro dake karamar hukumar Dan-musa da rashin yin aikin daya dace da kuma jin tsoron yan’ bindiga kamar yanda ya ambata a faifan bidiyon.

 

 

 

 

 

 

 

 

Comment(2)

  1. Dan majalissaar Dan musa ya fadi gaskiya domin ko a tsarin Constitution wayanda suka fi hada kuri’a su sukafi kowa cancantar su sha romon dimokaradiyya Amma sai aka saka mamu da kashe yan uwanmu a kullum saidai labaran iska ake in kuma an kamasu sai a tsaya anata sakarci Wanda kamata yayi ace definitely aka kama yan ta’adda kashesu kawai za’ayi Amma sai a tsaya wata shari’ar karya sai kace su wayanda aka kashe ba sunansu mutane ba

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: