Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Dandazon ya’yan jam’iyyar PDM sun koma APC a tafiyar Hambaliyya shiyyar Funtua
Dandazon ya’yan jam’iyyar PDM  sun koma APC a tafiyar Hambaliyya shiyyar Funtua

Dandazon ya’yan jam’iyyar PDM sun koma APC a tafiyar Hambaliyya shiyyar Funtua

0

Jikan Hambali Ya Karbi Ya’yan Tsohuwar Jam’iyar PDM A Shiyyar Funtua Da Suka Koma Tafiyar Hambaliyya.

Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina a zaben Shekarar 2019 a Karkashin Jam’iyar APC Alhaji Garba Dankani Jikan Hambali,ya karbi dumbin ya’yan tsohuwar Jam’iyar PDM da suka shigo Jam’iyar APC a Tafiyar Hambaliyya daga Shiyyar Funtua.

Wadanda suka shigo tafiyar ta Hambaliyya sun fito ne daga Kananan Hukumomi 11 dake Shiyyar ta Funtua.

An dai karbi ya’yan Jam’iyar ta PDM ne zuwa tafiyar Hambaliyya a karkashin wakilansu daga Kananan Hukumomin Shiyyar a lokacin wani taro da Jikan Hambalin ya gudanar da su a garin Funtua.

Da yake jawabi a lokacin tattaunawar,Alhaji Garba Dankani ya yabawa ya’yan Jam’iyar ta PDM akan yanke shawarar shigowa tafiyarshi domin samun nasara a zaben 2023.

Alhaji Garba Dankani yasha alwashin cewa zaya tafi da dukkanninsu ba tare da nuna banbanci ba tsakaninsu da tsofaffin ya’yan tafiyar ta Hambaliyya.

Ya kuma yi Kira a garesu akan kada su gajiya wurin yada manufofinshi na alkairi ga Jihar Katsina domin kara samun karbuwa daga jama’ar Jihar a zaben 2023.

Jikan Hambali yayi addu’a akan Allah SWT ya kawo karshen matsalolinda ke addabar Jihar Katsina da kasa baki daya domin samun karin cigaba.

A nasu jawabin jagororin Ya’yan Jam’iyar ta PDM da aka karba Alhaji Musa Abdullahi Omo Malumfashi da Alhaji Ahmad Alti Funtua sunce sunada yakinin Jikan Hambali adali ne shiyasa suka suka shiga tafiyarshi.

Sun tabbatarwa al’umar Jihar Katsina cewar Jikan Hambali ya chanchanci jagorantar Jihar lura da kwazonsh da jajircewa a dukkan abinda ya fuskanta don haka akwai bukatar jama’a su jarabashi domin ganin an gudu tare an tsira tare.

Sunce dubban magoya bayan PDM daga Kananan Hukumomi 11 na Shiyyar Funtua ne suka yanke shawarar shiga tafiyar ta Hambaliyya a cikin Jam’iyar APC.

Sun lashi takobin kasancewa masu biyayya ga tafiyar domin samun nasara a zabukanda ke tafe.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: