Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA 2023: Wata kungiya na son AIG Abdulkarim Dauda Daura ya fito takarar Gwamnan Katsina
2023: Wata kungiya na son AIG Abdulkarim Dauda Daura ya fito takarar Gwamnan Katsina

2023: Wata kungiya na son AIG Abdulkarim Dauda Daura ya fito takarar Gwamnan Katsina

1

Zaben 2023: Wata kungiya na son AIG Abdulkarim Dauda Daura ya fito takarar Gwamnan Katsina

Zaben 2023: An yi kira ga AIG Abdulkarim Dauda Daura ya fito takarar Gwamnan Katsina

Wata kungiya mai rajin kishi kasa da cigaba ta ‘yan asalin shiyyar Daura watau Daura Zone Concern Indigines Movement a turance ta yi kira ga babban jami’in rundunar yan sanda ta kasa kuma mataimakin Insifecta Janar, Abdulkarim Dauda Daura da ya fito takarar Gwamnan jihar Katsina a zaben 2023.

Wannan kiran dai ya fito ne ta hannun mataimakin kungiyar, Honorable Sa’idu Sulaiman Kofar Arewa Daura a wata sanarwar da suka fitar dauke da sa hannun sa a madadin sauran mambobin ‘yan kungiyar kuma jaridar Katsina Post ta samu.

A cikin sanarwar, kungiyar ta bayyana cewa: “La’akari da halin rashin tsaro da Jihar mu ta Katsina ta tsinci kanta ciki a halin yanzu, lalle akwai bukatar samun gogaggen masanin tsaro, adali kuma wanda ya samu kyakykyawar shaida daga al’umma, mai kishi kuma mai tausayin na kasa dashi, wanda baya kyashin fitar da dukiyarsa don tallafama talaka, mutum mai son hidimtawa tare da son cigaban matasa”.

Kungiyar ta cigaba da cewa hakan ne ma yasa ta zakulo AIG Abdulkarim Dauda a bisa cancantarsa kuma take kira gareshi da babbar murya da yazo ya jagoranci jihar ta Katsina don tsamo ta daga halin da take ciki.

“A laluben mai irin wadancen halayen ne wannan kungiyar ta yanke shawarar kara jaddada kira ga AIG Abdulkarim Dauda ya fito neman takarar kujerar Gwamnan jiharmu ta Katsina a shekarar 2023 mai zuwa.

“Mun yanke wannan shawarar kira a gareshi ne, bisa la’akari da alkhairan dake tattare da wannan bawan Allah.

“Muna da bayanai na irin hidimar da yake ma addini da kuma musamman yadda yake janyo matasa a jikinsa tareda tallafa masu da nema masu ayyukan da za suyi dogara da kawunansu, hakika mutum ne jarimi da baya barin ko ta kwana wajen abinda ya shafi taimaka ma duk wanda har matsalarsa takai gareshi ko kukan sa ya kai ga kunnuwansa.

“An tabbatar AIG Abdulkarim mutumin kirki ne, ga duk Wanda wata mu’amula ta taba hada su, to shi shaida ne akan hakan. Alkhairansa ba wani boyayyen al’amari bane ya kai ko’ina a fadin jiha.

“Hakika a dai dai wannan lokaci Jama’ar Jihar katsina na bukatar gudumawarsa domin haka ne yanzu ya zame masa wajibi ya amsa kiran al’umma Jihar Katsina yadawo gida dan hidimtawa al’ummar jiharasa.

“Wajibi ga AIG Abdulkarim Dauda da zarar wannan kira ya kai gareshi, dole ne ya amsa kira ba tare da bata lokaci ba, saboda rashin amsa wannan kira ba zai yi ma al’ummar jihar Katsina dadi ba.

“Allah SWT ya taimaki Jihar Katsina ya bawa Mai girma gwamna Aminu Bello Masari damar karasa wa’adinsa cikin nasara da aminci.

“Allah ya raya mana jiharmu ta katsina ya zaba mana shuwagabanni adalai ameen.”

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: