Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Wani dan bindiga ya gindaya sharadin samun zaman lafiya a Katsina
Wani dan bindiga ya gindaya sharadin samun zaman lafiya a Katsina

Wani dan bindiga ya gindaya sharadin samun zaman lafiya a Katsina

0

Wani dan bindiga ya gindaya sharadin samun zaman lafiya a Katsina

Daga ciki ya bayyana dole a dawo masa da matansa guda biyu dake hannun yan sanda

Wani sananne kuma gogaggen dan bindiga da ya shahara a nan jihar Katsina mai suna Usman Idris, da aka fi sani da ‘Ruga Kachallah’ wanda ya addabi yankin karamar hukumar Safana ya bada sharuddan dawo da zaman lafiya a yankin nasa.

Kamar yadda Katsina Daily Post News ta karanta firar da Premium Times ta yi da shi, ya bayyana cewa dole sai Gwamnati ta biya shi buhunan hatsinsa guda 100 da rugarsa da aka kone tare da sako masa matasan guda biyu da yan sanda suka tafi da su bayan yan sanda sun kune masa ruga.

Haka kuma Kachalla ya ce akwai dakarunsa da aka kama wadanda suke yi masa aikin gona ba yan ta’ada bane suma, yana bukatar da a sako masa su, madamar ana son zaman lafiya ya dawo a yankin na Safana.

A yanzun haka akwai kauyuka irinsu; Tulumbusawa, ‘Yartsaku, Makera, Gimi da Chirena dake karkashin ikon Kachalla, dake karkashin ikonsa wajen dole sai sun nemi izinin zuwa gona.

Sai dai rundunar yan sandan jihar Katsina ta bayyana Kachalla a matsayin wanda ya tada tuba har kusan sau hudu, don haka ko yanzun idan a Karan kansa ne ya nuna zai tuba ya aje makamai ana maraba da shi kamar yadda SP Gambo Isa ya yi wa majiyar tamu Karin haske.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: