Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Tarihin Masarautar Daura Da Jerin Sarakunan Ta 42
Tarihin Masarautar Daura Da Jerin Sarakunan Ta 42

Tarihin Masarautar Daura Da Jerin Sarakunan Ta 42

1

Tarihin Masarautar Daura Da Jerin Sarakunan Ta 42

Gabatarwa

Tun farkon kafuwar masarautar Daura zuwa yau, ta yi sarakuna sittin (60), tun daga kan Abduldari, mutumin da ya taso daga Gabas ta tsakiya ya fara kafa ita masarautar ta Daura a wani Dausayi da ake kira ‘Gigiɗo’ kamar yadda ya zo a Littafin Taƙaitaccen Tarihin Daura wanda Fadar Mai Martaba Sarkin Daura ta wallafa.

Sai dai, akwai wata matsala babba guda ɗaya ta rashin samu cikakken jerin sunayen sarakunan na Daura tun daga dauri zuwa yau. Saboda ko shi ma wakilin Tarihi malam Mamman Siya Abubakar cewa ya yi “…Ba mu da cikakken tarihin Daura daga lokacin kafuwar mulki, sai bayan jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da ya auku a farkon ƙarni na sha tara…”

Saboda haka ga ɗan abin da ya samu dangane da jerin sunayen sarakunan Daura.

Rukunin Sarakunan Farko

1. Abduldari
2. Kufuru.
3. Gino
4. Yakumo
5. Yakunya
6. Walzamu
7. Yanbamu
8. Gizirgizir
9. Innagari
10. Daurama
11. Gamata
12. Shata
13. Batatuma
14. Sandamata
15. Jamatu
16. Hamata
17. Zama
18. Shawa
19. Bawo

Rukunin Sarakuna na Biyu, Sarakunan Fulani

20. Malam Isiyaku
21. Malam Yusufu
22. Malam Muhammadu Sani
23. Malam Zubairu
24. Malam Muhammadu Bello
25. Malam Muhammadu Altine
26. Malam Muhammadu Mai Gardo
27. Buntarawa Sogiji
28. Magajiya Murnai

Rukunin Sarakunan Haɓe,
Tun daga Masu gudun Hijira har zuwa yau

29. Sarkin Gwari Abdu (Abdullahi)
30. Sarki Lukudi ɗan Tsoho
31. Sarki Nuhu ɗan Lukudi
32. Sarki Mamman Sha ɗan Sarkin Gwari Abdu
33. Sarki Haruna ɗan Sarki Lukudi
34. Sarki Ɗan’aro ɗan Sarkin Gwari Abdu
35. Sarki Tafida ɗan Sarki Nuhu
36. Sarki Sulaiman ɗan Sarkin Gwari Abdu
37. Sarki Yusufu ɗan Sarki Lukudi
38. Sarki Tafida ɗan Sarki Nuhu (a Karo na biyu)
39. Sarki Musa ɗan Sarki Nuhu
40. Sarki Abdurrahman ɗan Sarki Musa
41. Sarki Muhammadu Bashar
42. Sarki Umar Faruq Umar

Manazarta:

Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.

Sai kuma tattaunawa da Wakilin Tarihin na Daura da kuma Dogarin Sarkin Daura mai suna Ɗandaushe, a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: