Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Masari Ya Ciwo Karin Bashin Naira Biliyan 50 Don Yin Wasu Ayyuka
Masari Ya Ciwo Karin Bashin Naira Biliyan 50 Don Yin Wasu Ayyuka

Masari Ya Ciwo Karin Bashin Naira Biliyan 50 Don Yin Wasu Ayyuka

1

Masari Ya Ciwo Bashin Naira Biliyan 50 Don Kammala Wasu Ayyukan Sa

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kammala shirye-shiryen ta domin karbo bashin Naira biliyan 50 daga gwamnatin tarayya domin kammala wasu ayyukan da ake yi a jihar da kuma fara yin wasu.

Kwamishinan kasafin kudi da tsare tsare, Hwanarabul Farouk Jobe shine ya bayyana hakan lokacin da yake magana a wurin taron wayar ma al’umma kai akan kasafin kudin da ake shiryawa na 2022 a dakin taro na tsohon gidan Gwamnati ranar Alhamis din da ta gabata.

A cewar Kwamishinan, tuni har gwamnatin ta tarayya ta amince da kudurin na gwamnatin jihar.

Hwanarabul Jobe ya kara da cewa ayyukan da gwamnatin ta kuduri aniyar idawa da kudin sun hada da gyaran madatsar ruwan Ajiwa, da ayyukan jawo ruwan dam din Zobe.

Sauran, kamar yadda yace sun hada da gyaran wasu hanyoyi na jihar da kuma kammala gyaran asibitocin da gwamnatin ke yi.

Haka zalika Hwanarabul Jobe ya ce duk a cikin kudin, gwamnatin jihar za ta yi hanyar kasa ta zamani a cikin garin Katsina a shatale-talen Kofar Kaura da Kofar kwaya.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: