Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Latest Kare Kai: Tata yace Gwamna Masari ya bada kudin siyen makaman in da gaske ya keyi
Kare Kai: Tata yace Gwamna Masari ya bada kudin siyen makaman in da gaske ya keyi

Kare Kai: Tata yace Gwamna Masari ya bada kudin siyen makaman in da gaske ya keyi

1

Kare Kai: Tata yace Gwamna Masari ya bada kudin siyen makaman in da gaske ya keyi

Tsohon dan takarar Gwamna a jam’iyyar APGA zaben 2015, Alhaji Umar Abdullahi Tata ya yi tsokaci game da kiran da Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari yayi na mutane su tashi su kare kan su daga ‘yan bindiga.

Tatan yayi wannan tsokacin ne a cikin wata doguwar budaddiyar wasika da ya rubutawa Gwamnan ta kafar sadarwar zamani ta Facebook a ranar Larabar da ta gabata.

A cikin wasikar, Tata ya bayyana cewa kamata yayi Gwamnan ya fitar da kudin gwamnati ya ba kananan hukumomin da matsalar tsaron ta fi shafa domin su siya makamai indai har da gaske yake yi.

Ga dai wasikar nan da ya rubuta:

KIRA GA MAI GIRMA GWAMNA AMINU BELLO MASARI A KAN KIRAN DA YAYI NA CEWA MUTANE SU KARE KANSU

Na dade ban shiga manhajar Facebook ba amman akwai bukatar inyi tsokaci a kan wannan kira da gwamna yayi na cewa mutane su dauki makamai domin kare kawunan su daga wannan bala’i na tsaro da ya addabi kowa.

Ya mai girma gwamna ina son ka sani daman can mutane ba zaune suke ba kamar tumakai ana kashe su a banza ba, a a suna bakin kokarin su domin kare kawunan su a daidai gwargwadon kafin su. Abin ne yafi kafin su saboda su wadannan barayin suna da miyagun makaman da ko jami’an tsaro basu dasu.

Ta ina mutanen da suka fi karfin jami’an tsaro zamu iya tunkarar su da cizo, bakan danko ko kuma bindigar toka? In har da gaske kake ya mai girma to ga shawara.

Na farko Allah ya tattara dukiyar jihar Katsina gaba dayanta ya saka ta a karkashin ka to kayi amfani da dukiyar nan don taimaka ma rayuwar bayin Allah, ka sai ma jami’an tsaro motocin aiki don basu dasu kuma da dama tun wadanda gwamnatin Shema ta sai masu ne suke fama dasu yanzun. In kayi wannan sai kayi kokari, ya mai girma a karkashin jagoranci gwamnati, ka hada kungiyar tsaro da ta kunshi Hakimai, malaman addini, yan sa kai, Matasa da masu fada aji a kowace local government da wannan bala’in ya addaba, ka basu gudummuwar N70m kowace local government su sayi makamai da abubuwan hawa. Sannan kamar yanda ka dauki yan S-Power aiki ka dauki yan banga 5000 aiki ka basu albashi don karfafa su akalla mutum 500 per most affected and frontline local government ka basu abin hawa da makamai kaga in akwai dan iskan barawon da zai kara satar wani ko kashe rai a jihar Katsina.

Dadi bisa wannan, ya mai girma sai kuma ka bada general amnesty ga yan sakai din da sukayi artabu da barayi suka sami galaba a kansu amman daga baya jami’an tsaro suka bisu har gida suka kamo su. Ni sheda ne kuma na nemi taimakon ka da Attorney General a kan irin wannan matsalar ban samu ba. Ina tabbatar maka ya mai girma gwamna daga cikin wadannan mutanen da aka kama don sun kashe barayi wasunsu an yanke masu hukuncin kisa, wasu suna gidan yari wasu kuma har yanzun suna ta zarya a kotu. In dai da gaske kake cewa mu kare kawunan mu to ka fara da janye sharia da wadanda suka kare mu.

Inda hali ya mai girma gwamna wannan umurnin naka ka maida shi DOKA a kai shi State Assembly suyi passing nashi into law don gudun abinda ka iya zuwa ya dawo tsakanin mu da jami’an tsaro tunda maganar ka kadai ba zata zama hujja a kotu ba.

Na san Katsina an sami kudin Paris Club so babu dalilin da zai sa mutane su sayar da gidaje da gonakin su don sayen makamai bacin akwai kudi a jiha da za a iya wannan aikin.

Sannan daga karshe ya mai girma gwamna duk uzurin da Bakatsine zai yi maka yayi maka to ina baka shawara da kaji tsoron Allah don Ya san abinda ka boye!

Allah ka bamu zaman lafia a jihar mu da kasa baki daya!

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: